Mai shari’a Abiola Sholadoye na kotun laifuffukan jima’i da cin zarafin cikin gida a Jihar Legas ta tasa keyyar wani dattijo mai shekaru 43, Augustine Ekerette har gidan yarin Kirikiri bisa zarginsa da lalata da agolarsa mai shekaru 17 tare da yi mata ciki.
Ana zargin wanda ake tuhuma da aikata laifin tsakanin shekarar 2020 zuwa Yuli 2023 a gida mai lamba 124, GRA Ogunla a yankin Ikorodu na jihar.
- Xi Zai Halarci Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
- Wane Ne Ke Tallafa Wa Jam’iyyun Siyasar Nijeriya Da Kudade?
Mai gabatar da kara, Ms Adejoke Bolade, ta shaida wa kotun cewa, wanda ake zargin ya ci gaba da tozarta yarinyar mai shekaru 17 da haihuwa ta hanyar yin lalata da ita ba bisa ka’ida ba.
Bolade ta kuma nanata cewa laifin ya ci karo da sashe na 137 na dokar laifuka Cap C.17, Bol. 3 Dokokin Jihar Legas na 2015.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin. Dangane da rokonsa, mai gabatar da kara ya bukaci kotun da ta sanya ranar da za a fara shari’ar. Daga nan ne alkalin ya dage sauraren karar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba domin shari’a.
An karanta laifin da ake tuhumar wanda ake karar kamar haka: “Augustine Ekerette, tsakanin shekarun 2020 zuwa Yuli 2023 a Plot 124, GRA Ogunla Ikorodu, a sashin shari’a na Ikeja, ka ci gaba da tozarta wata matashiya mai suna Odili Patience mai shekaru 17, ta hanyar aikata jima’i na haram da ita, wanda hakan ya saba da sashe na 137 na dokar laifuka Cap C.17, Bol.3 Laws na Jihar Legas, 2015.”