Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta tabbatar da cafke Kwamishinan Ayyuka na Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara, bisa zarginsa da aikata lalata da wata matar aure.Â
Darakta Janar na Hisbah, Abba Sufi, ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan korafin da mijin matar ya shiga a gaban hukumar tasu.
- Sin Ta Fara Amfani Da Tauraron Dan Adam Wajen Duba Manyan Hanyoyin Wutar Lantarki A Karo Na Farko
- Kashi 67 Cikin 100 Na Ɗaliban Kaduna Sun Samu Nasara A WAEC – Kwamishinan Ilimi
Mijin matar, Nasiru Bulama, ya shigar da korafi a Hisbah da sauran hukumomin tsaro kan zargin da yake wa matarsa da yin lalata da Kwamishinan.
Hisbah ta tabbatar da zargin da mijin ke yi wa matarsa mai suna Tasleem Baba Nabegu ne, bayan da suka kama kwamishinan, wanda ya tabbatar musu da yin lalata da matar.
Abba, ya ce za su gurfanar da Kwamishinan a gaban kotu a ranar Litinin 21 ga watan Oktoba, 2024.