Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da wasan kwaikwayo da rudanin shari’a da ke tattare da gazawar jami’an tsaro wajen cafke Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, duk da kokarin da aka yi.
Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasar, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana a wani shirin zamantakewa da tattalin arziki na gidan talabijin na Channels, mai suna ‘Inside Sources with Laolu Akande’.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- MDD Za Ta Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Taimaka Wa Nijeriya Kawo Karshen Talauci
Onanuga ya bayyana kalubale na musamman da ke tattare da kusancin Bello da magajinsa, Gwamna Usman Ododo, wanda ke da kariyar tsarin mulki.
LEADERSHIP ta tunatar da cewa, a watan Afrilu, Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa ana neman Bello ne bisa zarginsa da aikata laifukan kudi da suka hada da Naira biliyan 80.2. Duk da cewa hukumar EFCC ta yi yunkurin cafke tsohon gwamnan, amma yunkurin ya ci tura, inda rahotanni suka ce Ododo ya kare Bello tare da ba wa gwamnan mafaka a masaukinsa.
Ya kara da cewa, yayin da hukumar EFCC ta dukufa wajen gurfanar da Bello a gaban kuliya, kariyar da aka bai wa Gwamna Ododo a karkashin tsarin mulki na dagula duk wani yunkuri na kama tsohon gwamnan.
Ya ci gaba da cewa, “Wannan ita ce matsalar domin idan shi (Bello) ya zauna a gidan Gwamna Ododo, ‘yan sanda ba za su iya yin komai ba saboda za su keta wannan rigar da gwamna ke da ita.
“Kamar jami’in diflomasiyya ne da yake da kariya, don haka ba za ku iya yin komai game da shi ba. Kun tuna a Burtaniya lokacin da suke neman mutumin nan Wikileaks, sai ya je ya buya a wani ofishin jakadanci a Biritaniya, ba abin da su ( jami’an tsaro) za su iya yi, dole haka nan suka bar shi a can. Ina tsammanin daga baya ne ya fito suka kama shi,” Onanuga ya fadi haka yayin da yake tabbatar da rashin ikon EFCC.
Tsohon gwamnan Jihar Kogi, wanda ya yi mulki daga shekarar 2016 zuwa Mayu 2024, ya kasa gurfana a gaban kotu duk da yawan sammaci da kuma dage sauraren karar da aka yi masa.