A ranar Asabar 4 ga watan Yuni shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai halarci wani taro na musamman na kungiyar ECOWAS a birnin Accra na kasar Ghana kan harkokin siyasa a kasar Mali da sauran sassan yankin.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, taron da zai gudana a fadar shugaban kasa da ke babban birnin Accra, wanda aka fi sani da gidan Jubilee, ana sa ran zai duba irin ci gaban da gwamnatin mulkin sojan kasar ta Mali ta samu kan mayar da kasar bisa tafarkin demokradiyya.
Shugabannin kasashen za su kuma duba halin da ake ciki a Jamhuriyar Burkina Faso da Guinea.
Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno (rtd) da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar.
Bayan kammala taron zai koma Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp