Gwamnatin Jihar Gombe ta kaddamar da kwamiti mai mambobi 7 don rabawa da sayar da takin zamani na daminar bana ga manoman jihar domin saukaka wa manoma wajen samun Takin cikin sauki.
Lokacin da yake kaddamar da kwamitin ranar Alhamis a madadin Gwamnan Jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bukaci kwamitin ya tabbatar da rabawa da sayar da takin akan lokaci ga manoma jihar.
- Ministar Jin Kai Ta Raba Wa Mata 3,500 Tallafin Kudi A Gombe
- Gwamnatin Gombe Za Ta Tallafa Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Funakaye
Sakataren ya ce ‘yan kwanaki bayan kaddamar da sayar da takin da gwamnan jihar ya yi a hukumance, gwamnatin jihar ta samo taki tirela 120, kimanin buhu dubu 72 kenan don rabawa manoman jihar.
“Aikin da aka daura muku ba wani mai wuya ba ne; karbar takin gwamnatin jihar tirela 120, da sanya ido wajen rarrabawa da sayar da shi a dukkan matakai, da kuma bai wa gwamnati shawarwarin da suka dace kan aikin da aka daura muku”. Cewar Sakataren gwamnatin Jihar.