Rundunar ’Yansandan Jihar Kogi ta tabbatar da sace ’yan uwa uku na tsohon Editan Daily Trust, Malam Ahmed Ajobe, ciki har da ƙanwarsa, Halimtu-Sadiya Tahir.
An sace su ne a ranar Alhamis a hanyar Ankpa-Adoka-Makurdi da ke cikin ƙaramar hukumar Ankpa, yayin da suke dawowa daga kasuwa a wani ƙauye kusa da Awo.
- Manomanmu Sun Tabka Asarar Sama Da Naira Miliyan 100 A Harin ‘Yan Bindiga – Dan Majalisa
- ‘Yan Bindiga Sun Kone Gonakin Manoma A Zamfara
Kakakin ’Yansandan Jihar Kogi, William Aya, ya bayyana cewa DPO na yankin ya tura jami’ansa don ceto waɗanda aka sace. Haka kuma, Kwamishinan ’Yamsanda, Bethrand Onuoha, ya umarci tawagar ’yansanda na musamman da su ƙarfafa aikin ceto a yankin. Aya ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa don ganin an Kuɓutar da waɗanda aka sace tare da gurfanar da masu laifin a gaban shari’a.
Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi fansar Naira miliyan 50 don sakin su. Wani ɗan uwansu, wanda ya zabi a sakaye sunansa, ya ce lamarin ya faru ne yayin da waɗanda aka sace suka je kasuwa domin siyan kayan shirin addu’ar kwana bakwai na mahaifiyar Ajobe, Malama Aishetu Tahir, wadda ta rasu a ranar Lahadi sakamakon rashin lafiya.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu babu wani kuɗin fansa da aka biya, kuma waɗanda aka sace suna can.