Gobara ta tashi a ranar Laraba a sashen gidan rediyon Nijeriya da ke kan titin Ikoyi, a Jihar Legas.
Gobarar, ta tashi da misalin karfe 5:30 na yamma, amma jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jihar Legas suka shawo kanta.
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
- Liverpool Ta Sake Nuna Barakar Real Madrid A Anfield
Daraktar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Margaret Adeseye, ta ce gobarar ta yi tsanani saboda irin kayan da ke cikin sashen gidan rediyon.
Sai dai kokarin da jami’an suka yi ya taimaka wajen hana wutar zuwa wani sashen.
Ba a samu rahoton asarar rai ba, kuma har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Jami’an kashe gobara na ci gaba da aiki don tabbatar da kashe gobarar gaba daya.