Jagorancin Alhaji Bashir Adewale Adeniyi a matsayin Shugaban Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), ya kawo sauye-sauye masu matuƙar tasiri, inda ya samar da zaman lafiya da inganta aiki da ƙaruwar kuɗaɗen shiga. Wannan nasara ta taimaka matuƙa wajen bunƙasar tattalin arziƙin Nijeriya, wanda ya sa aka zaɓe shi a matsayin Gwarzon Ma’aikaci Na Shekarar 2024.
Tun bayan naɗa shi muƙamin a watan Yunin 2023, Adeniyi ya fuskanci manyan matsaloli a hukumar, wanda suka haɗa da rashin ƙwarewar aiki da cin hanci da rashawa, da tsofaffin hanyoyin aiki. Ta hanyar amfani da hangen nesa da ƙwazo, ya bijiro da sababbin tsare-tsare a hukumar, wanda ya nuna yadda za a iya kawo gyare-gyare masu kyau a ɓangaren ayyukan gwamnati a Nijeriya.
- Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters
- Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke
Dabarun Adeniyi sun fi mayar da hankali kan sauƙaƙa ayyukan Kwastam da kuma inganta kasuwanci.
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyensa shi ne rage yawan tawagar da hukumar ke da su, inda ya haɗe rundunar Strike Force Teams da Federal Operations Unit (FOU). Wannan ya rage yawan shingen bincike daga biyar zuwa biyu a kowace hanya, wanda ya sauƙaƙa harkokin kasuwanci kuma ya rage cin hanci a kan iyaka. Wannan gyara ya ƙara wanzar da gaskiya a aikin hukumar tare da tallafa wa kasuwanci, inda ya kafa sabon mizanin inganta aiki.
A ƙarƙashin shugabancinsa, hukumar NCS ta ƙarfafa haɗin guiwar ƙasa da ƙasa, musamman da Ƙungiyar Kwastam ta Duniya (WCO), don tabbatar da amfani da kyawawan ƙa’idojin aiki na ƙasa da ƙasa. Adeniyi ya kuma mayar da hankali kan tsaro a iyakokin ƙasa ta hanyar samar da sabbin dabaru, kamar sayen jirgin sama ƙirar Cessna Grand Caravan EX-208B domin bincike ta sama. Wannan jirgin ya inganta aikin sintiri a wuraren da ke da wahalar zuwa, wanda ya bunƙasa yaƙi da safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba.
Sabunta fasaha shi ma wani ginshiƙi ne a jagorancin Adeniyi. Ya jagoranci shirye-shirye irin su Authorized Economic Operators (AEO), wanda ya sauƙaƙa aikin Kwastam ga ‘yan kasuwa masu bin doka tare da ƙara musu damar yin gogayya a kasuwannin duniya.
Ƙaddamar da Time Release Study (TRS) da amfani da fasahar geospatial ya ƙara tabbatar da jajircewarsa wajen amfani da fasaha domin inganta aiki da samun sahihanci.
Waɗannan sauye-sauye sun haifar da sakamako mai tasirin gaske a fannin tattalin arziƙi. Kuɗaɗen shiga na wata-wata sun ƙaru da kashi 70.13, daga Naira biliyan 202 zuwa sama da Naira biliyan 343.
A shekarar 2023, duk da ragi da aka samu a harkokin kasuwanci, hukumar ta samu jimillar kuɗin shiga har Naira tiriliyan 3.2, wanda hakan ya ƙaru da kashi 21.4 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wannan ya nuna cewa Adeniyi ya inganta kuɗaɗen gwamnati ta hanyar samar da tsari mai inganci.
Bugu da ƙari, Adeniyi ya ƙara ƙarfi a ɓangaren aiwatar da dokoki. A shekarar 2023 kaɗai, hukumar ta kama kayayyaki 1,763 da darajar kuɗinsu ta kai Naira biliyan 11.9 a matsayin kuɗin haraji, tare da gurfanar da mutane 52. Wannan tsauraran matakai sun ƙara tabbatar da sadaukarwarsa wajen kare tattalin arziƙin Nijeriya daga illolin safarar kayan haram.
Duk da waɗannan nasarori, Adeniyi ya ci gaba da duba yadda zai ƙara inganta harkokin kasuwanci. Burinsa na gaba ya haɗa da samar da sabbin dabarun aiki a iyakoki, gyara tsarin TRS da shirye-shiryen AEO, tare da rage jinkiri a harkokin gwamnati.
Haka kuma yana ƙoƙarin wayar da kan jama’a kan illolin da safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba ke yi wa tattalin arziƙi, tare da tabbatar da Nijeriya ta samu matsayi mai kyau a kasuwannin duniya.
Jagorancin Adeniyi ya zama misali a tsakanin shugabannin ma’aikatun gwamnati, wanda hakan ya sa ya cancanci wannan lambar yabo daga Jaridar Leadership