Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa za a tsawaita tsawon lokacin kasafin kuɗin shekarar 2024 zuwa ranar 25 ga watan Yunin 2025.
Ya bayyana haka ne cikin jawabinsa na buɗe taron gabatar da kasafin 2025 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, zai yi a zauren majalisar da ta haɗa da ‘yan majalisar Dattijai da ta Wakilai a yau Laraba 18/12/2024.
A cewarsa, kaso 50 ne na kasafin kuɗin shekarar 2024 ya aiwatu, inda ya bar giɓin kaso 50 da bai aiwatu, don haka, akwai buƙatar tsawaita lokaci don aiwatar da shi yadda ya dace.