An kaddamar da babban taro a kan magance korafe-korafen al’umma na birnin Beijing na shekarar 2024 a birnin, yau Laraba, mai taken “Zamanantarwa domin shugabanci mai fifita al’umma a birane”.
Wanda yake kunshe da mutane fiye da miliyan 21, babban birnin kasar ta Sin Beijing, ya bullo da sauye-sauye a kan magance korafe-korafen al’umma ne a watan Janairun shekarar 2019, ta hanyar amfani da layin kiran waya na gaggawa mai lambobin 12345.
A fiye da shekaru shida da suka gabata, layin wayar ya karbi korafe-korafen mutane miliyan 150, inda kason magance korafe-korafen ya karu daga kashi 53 zuwa kashi 97 cikin dari, kana nuna gamsuwar jama’a kan yadda aka magance masu korafe-korafen, ya karu daga kashi 65 zuwa 97.3 cikin dari, kamar yadda darektan hukumar kula da mulkin birnin Beijing da tattara bayanai, Shen Binhua ya bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)