• English
  • Business News
Saturday, September 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

PRP Ta Tabbatar Da Tattaunawar Hadewa Da Jam’iyyar ADC Gabanin Zaben 2027

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
9 months ago
in Labarai
0
PRP
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jam’iyyar PRP ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da wata jam’iyyar adawa ta ADC, kan yuwuwar hadewar jam’iyyun gabanin babban zaben shekarar 2027.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello ne ya bayyana hakan a wani taron hadin gwiwa da takwaransa na ADC, Ralph Nwosu a Abuja.

  • Da Rancen Naira Tiriliyan 13 Za A Cike Gibin Kasafin Kudin 2025 — Edun
  • Kisan Jami’an ‘Yansanda 229 A Cikin Wata 22 Babbar Musiba Ce Ga Kasa

Matakin na zuwa ne kwanaki uku bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta yi gargadin cewa babu wani hadewar shugabannin ‘yan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, da zai iya kwace kujerar Shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.

Jam’iyyar APC na mayar da martani ne kan kalaman da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya yi cewa shugaban nasa da takwaransa na jam’iyyar LP duk sun koyi darasi a zaben da ya gabata, kuma za su hada kai domin korar jam’iyya APC a kan karagar mulki.

Haka zalika, wasu jam’iyyun siyasa na adawa a karkashin inuwar hadakar jam’iyyun siyasa da jam’iyyar SDP, su ma sun bayyana shirinsu na tattaunawa kan yiwuwar yin kawance, suna masu cewa kasar na bukatar hadakar Atiku da Obi.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma’a, Bello ya tabbatar da cewa tuni suka fara tattaunawa da shugabannin ADC domin fara shirin ceto kasar nan daga hannun jam’iyya mai mulki.

Ya ce, “Eh, mun fara tattaunawa. Ba ma tsoron hadewa gaba daya. Mu duba tarihin zabe. PRP ita ce jam’iyyar siyasa mafi tsufa a yau. Mun kafa gwamnati a Kaduna a shekarar 1979, saboda kawancen siyasa da jam’iyyun UPN, NPP, da PNP a jihar.

“Idan sauran jam’iyyu suna son shiga cikinmu, to muna maraba da su. Kofofinmu a bude suke ga kowa da kowa hatta daidaikun mutane, ba jam’iyyun siyasa kadai ba. Amma idan sun gwammace su shiga jam’iyyar da ba ta son jama’a da maganar kudi kawai, su koma PDP da APC. Abin da suka tsaya a kai kenan.

“Don haka muna cewa mun gaji kuma muna son wani sabon sauyi. Idan kuma hakan ya bukaci ni ko shugaban jam’iyyar ADC ya sauka daga mukaminsa, to haka ya kasance. Wannan kasa ta fi mu muhimmanci. Kundin tsarin mulkin jam’iyyar PRP yana wakiltar ka’ida da akidar da muke tsayawa a kai.”

Nwosu ya kuma ce bukatar a hada kai ta kara samun karbuwa sakamakon gano cewa suna da akida daya.

Shugaban jam’iyyar ADC ya bayyana cewa, a halin da ake ciki wahalhalun da ake fama da su a kasar nan bai kamata a ce jama’a sun gaji ba, kuma suna bukatar sabon sauyi.

“Hadin kai da hadin gwiwa wanda a karshe zai haifar da yuwuwar hadaka yana gudana tsakanin PRP da ADC. Me ya sa muke yin haka? gina akidar siyasa da fayyace hangen inda muka dosa.

“Jam’iyyunmu ne suka fara wannan magana ta kawance, ba wai ta mutanen da ke neman mukami ba ne. Wadannan shugabannin jam’iyyun siyasa ne wadanda suke jin cewa ya kamata a samu sauyi a kasar nan kuma suna son ci gaba. A karshe, idan mutanen da ke neman mukami sun shigo dole ne su bi wasu ka’idojin da ya kamata su bi. Damuwarmu game da dimokuradiyya a fili take,” ya kara da cewa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Bai Kamata Kungiyar EU Ta Biyewa Masu Burin Rusha Alakarta Da Sin Ba

Next Post

Ya Kamata Amurka Ta Janye Cuba Daga Jerin Kasashe Masu Goyon Bayan Ta’addanci

Related

Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa
Labarai

Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

8 minutes ago
Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno
Labarai

Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

2 hours ago
Labarai

Ilimi Shi Ne Matakin Nasarar Rayuwar Duniya Da Lahira – Yerima Shettima

5 hours ago
NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai
Manyan Labarai

NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai

5 hours ago
Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya
Labarai

Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya

8 hours ago
Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 
Labarai

Ana Ci Gaba Da Caccakar El-rufai Kan Kalamansa Game Da Tsaron Kasa

17 hours ago
Next Post
Ya Kamata Amurka Ta Janye Cuba Daga Jerin Kasashe Masu Goyon Bayan Ta’addanci

Ya Kamata Amurka Ta Janye Cuba Daga Jerin Kasashe Masu Goyon Bayan Ta’addanci

LABARAI MASU NASABA

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

September 6, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

September 6, 2025
Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

September 6, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Kungiyoyi Da Abokan Arziki Na Ci Gaba Da Taya Dantsoho Murna

September 6, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Rudani Ya Kunno Kai Yayin Da INEC Ta Ki Amincewa Da Shugabancin ADC

September 6, 2025
Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC

Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC

September 6, 2025

Ilimi Shi Ne Matakin Nasarar Rayuwar Duniya Da Lahira – Yerima Shettima

September 6, 2025
NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai

NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai

September 6, 2025
Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya

Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya

September 6, 2025
Sashen Cinikayyar Bayar Da Hidima Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni Bakwai Na Farkon Shekarar Bana

Sashen Cinikayyar Bayar Da Hidima Na Sin Ya Bunkasa Cikin Watanni Bakwai Na Farkon Shekarar Bana

September 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.