Masu iya magana kan ce, duniya rawar ‘yan mata, ta gaba sai ta koma baya. Wani masanin halayyar Dan’adam kuma, Mista Lachlan Brown, ya ce rayuwa kamar rawa ce, ya kamata mutum ya san yaushe ya kamata ya matsa zuwa gaba, yaushe zai koma baya ko kuma wane lokaci ya dace ya tsaya cik! Gaba daya. A nan, abin da masanin yake nufi da tsayawa, “SHIRU”
Ba shi kadai ba, fannin nazarin halayyar Dan’adam shi ma ya goyi bayan haka. Akwai wani yanayi da mutum zai shiga na bacin rai, babban abin da ya fi dacewa ya yi a lokacin shi ne ya kame harshensa ga barin magana, kamar yadda Hausa suka ce, “Shiru ma amsa ne”.
- Mutum 10 Sun Mutu A Turmutsutsin Rabon Shinkafa A Abuja
- Bangarorin Da Suka Fi Samun Kaso Mai Tsoka A Kasafin Kudin 2025
Bari mu nausa mu gani, wadanne yanayi ne idan mutum ya tsinci kansa a ciki abin da zai yi mafi dacewa shi ne shiru.
1) Lokacin da mutum ya hasala
A yayin da hankali ya tashi, babu abin da ake yi sai daga murya cikin fushi, ko da iska tana kadawa a wurin mutum zai ji gumi ya rufe shi. To a irin wannan yanayi, ilimin halin Dan’adam ya ba da shawarar a ja baki a yi gum.
Kamar ba ka gamsu da hakan ba ko? To, tsaya ka ji. Bincike ya gano cewa idan mutum ya hasala, yanayin da yake shiga kan bata hanyoyin fitar da magana mai kyau da kuma yanke hukunci mafi dacewa a kan wani abu.
Ka ga, lokacin da muka hasala, kwakwalwarmu tana shiga cikin wani yanayi na fada ko dauke tunani mai kyau. Don haka muna iya fadin abubuwan da ba mu yi niyya ba ko kuma yanke shawarar da za mu yi nadama daga baya.
A matsayina na mai yin tunani kan abubuwa kafin aiwatarwa, zan iya ba da tabbacin cewa yin shiru a wannan lokacin shi ne mafi a’ala. Ta hanyar yin shiru, muna ba kanmu sararin mallakar zukatanmu ba tare da bari zucya ta debe mu mun yi abin da za mu yi da-na-sani ba.
Wannan shi ne ainihin jigon hankali, da yake nuna kana wurin da aka hasala ka amma kuma ka mallaki kanka ka kwantar da hankalinka ba tare da cewa uffan ba.
Don haka a gaba in ka sami kanka a cikin yanayin da ka hasala, ka ja dogon numfashi kuma ka zabi yin shiru a kan furta magana. Ba wai ana nufin ka yi shiru ka bar abin har abada ba, a’a, ana bukatar ka dan tsagaita ne tare da zabar hanya mafi dacewa da za ka mayar da martani cikin hikima da basira.
2) Lokacin da ba ka samu cikakken bayani kan wani abu ba
Yanayi na gaba da ya kamata ka yi shiru idan ka tsinci kanka a ciki maimakon surutu shi ne mafi dacewa da shiru amma kuma mutane suke yawan mantawa da shi. Idan ba ka da masaniya game da wani batu, zai fi kyau ka yi shiru maimakon hakikancewa kan karya ko rashin sani, wai ala dole kai ne ki-fadi.
Muna rayuwa ne a cikin zamani na bayyana ra’ayoyi da kuma iya tantance gaskiyar magana take yanke saboda fasaha. Yana da sauki mutum ya ji a ransa yana son tsoma baki a cikin komai, amma fa gaskiyar magana, bai dace ya zama koyaushe ba.
Wannan dabi’a ta tsoma bakia cikin komai jaraba ce, don haka mai yi, ya yi kokarin bari saboda zai rika fadar abubuwa ne da ba shi da cikakkiyar masaniya a kai. A karshe ya rudar da kansa da duk wanda yake sauraron sa.
Don haka, kar a manta, ba dole ne a komai sai mutum ya yi magana ba, ya ma fi kyau ka zamo mai sauraro don ka karu maimakon tsoma baki kan abin da ka jahilta.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa cikin yardar Allah