• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karuwar Cin Zarafi Da Makomar Yara A Nijeriya

by Ra'ayinmu
4 months ago
in Ra'ayinmu
0
Karuwar Cin Zarafi Da Makomar Yara A Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A kwanan baya ne, Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC) ta bayyana cewa, an  samu rahoton karin yawan  kananan yaran da aka yi watsi da su, wadanda suka kai sama da 1,300, tare da kuma take wasu ka’idoji.

Ofishin Sakataren Hukumar ne, ya bayyana shi wannan  rahoton a watan Oktoba na shekarar data gabata, inda rahoton ya nuna matukar damuwarsa kan karin yawan adadin yaran a cikin kowane wata daya.

  • Takardun Kuɗi Sun Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 4.8 Duk Da Ƙarancin Kuɗi A Nijeriya
  • Me Ya Sa Fursunoni Masu Jiran Hukuncin Kisa Ke Ƙara Cunkoso A Gidajen Yarin Nijeriya?

A kan wannan lamarin ne, wasu kwararru suka yi gargadin cewa, yin watsi da yaran, na kara yin kamari, inda kuma irin wadannan yaran ne, za su iya cin karo da fuskantar cin zarafin su, take hakkinsu da dai sauran wasu abubuwa.

Kazalika, rahoton Asusun tallafa wa  kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato (UNICEF), mai taken, “Matsayin Yara A Duniya A 2024” ya bayyana cewa, rayuwar yara ta nan gaba lalle tana a cikin hali na rashin tabbas.

Bugu da kari kuma, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, a sakonsa na bikin ranar yara ta duniya, ya bayyana kaduwarsa kan cewar, a wannan karnin na 21, abin takaici ne, ace, yara na zama a cikin yunwa, rashin samun ilimin zamani da kuma gazawar samar masu da kayan duba lafiyarsu.

Labarai Masu Nasaba

Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan

Bukatar Kawo Karshen Karin Kudin Kiran Waya Da Na Data

António ya ci gaba da cewa, abin kunya ne a ce, alummomin sun bar yara a cikin talauci da fadawa a cikin annoba.

Ya kara da cewa, makomar Nijeriya a yanzu da kuma ta nan gaba, ta dogara ne gabadaya a kan kulawa da rayuwar yara, inda ya sanar da cewa, babu wata tantama  da ake yi yara da matasa, sune manyan gobe, musamman ayi la’akari da cewa, sune suka fi yawa a cikin al’umma.

Sai dai kash! ana ci gaba da kalubalantar makomar Nijeriya, duba da yadda yara a kasar, suke ci gaba da fuskantar kalubale iri-iri na rayuwa, ciki har da yadda suke ci gaba da fuskantar talauci, fadawa a cikin rikice-rikice, rashin samun ilimin boko da kuma rashin samun kayan da za a duba lafiyarsu.

Wannan babban abin bakin ciki ne, ganin cewa, kashi 47 na yaran kasar sun kasance ‘ya’yan talakawa ne inda kuma kashi 67, ke a cikin nau’uin talauci

An kiyasta cewa, a watan Satumba na 2024, adadin yara masu shekaru daga shida zuwa goma sha hudu ne, wato miliyan 18.3, ba su zuwa makaranta.

Wannan adadin ya hada da, yara miliyan 10.2 da suka kamata ace suna zuwa makarantar Firamare ko ta Sakandare da suka kai adadin miliyan 8.1.

Kungiyar da ke kare ‘yancin yara a 2024, ta kiyast cewar yaran sun kai sama da yara ‘yan Nijeriya miliyan daya, na fuskantar rashin abinci mai gida jiki cikinsu har da yara miliyan 1.8, da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin samun abinci mai gina jiki.

Sai dai kuma, ana ganin cewa, wasu iyayen na yin watsi da ‘ya’yansu ne,saboda kalubale na matsin tattalin arziki da wasu ‘yan Nijeriya, ke ci gaba da fuskanta tare da kuma rashin samun wadataccen abinci.

Wannan matsalar ce, ta sanya wasu iyayen suka rungumi tsarin kayyade samun, musamman ma domin su samu damar ci gaba da daukar nauyin sauran ‘ya’yansu, da suka haifa

Asusun na UNICEF, ya bayyana cewa, nan da shekara ta 2050, a duk haihuwar daya a cikin haihuwa sha uku, da ta aka samu a Nijeriya, hakan na kara yawan adadin alummar kasar, wanda hakan ne kuma ke nuna karin wata bukatar, kara kulawa da yaran.

A saboda haka ne, ya kamata a gyara tsarin kayyade samun ciki, ba kawai shi tsarin ya kasance a matsayin wata magana ba, amma ko don saboda matsayin kulawa da lafiya da kuma kara bunkasa kasa.

Bugu da kari kuma, hakan zai iya taimakawa wajen samu daukar juna biyun da ba a shirya masa ba, da kuma magance sauran matsalolin kashe kudade.

Nijeriya za ta iya rage yawan yara miliyan 10.5, da suka daina zuwa makaranta zuwa kashi 90, idan har masu fada aji a kasar, sun rungumi tsarin samar da ilimin boko kyauta da kuma samar da damar samun duba lafiya kyauta.

Lokaci ya yi, da Nijeriya za ta dai na yin korafi a kan yawan adadin yaran da ba su zuwa makaranta, amma ta mayar da hankali, wajen lalubo da mafita, domina tabbatar da magance matsalar.

UNICEF ta bayar da shawarar cewa, ya kamata a zuba hannun jari a fannin ilimin zamani, musamman ma domin amfanin yaran.

A saboda haka ne, muke bada shawar vangarorin hukumomin tsaro da na shari’a na kasar, da su tabbatar da cewa, ana  hukunta masu cin zarafin yara.

Dokar kare hakkin yara (CRA), wadda ta zamo doka a 2003, ta tabbatar da ‘yancin, yara da shekarun su suka fara daga 18.

Hakanana ma, dokar ta kuma yi bayani a kan batutuwa masu dama, da suka hada da samar da kulawa da lafiyar yara, haramta yin auren wuri ga su ‘ya’ya mata da kuma gundunmawar da gwamnti za ta bayar ta kare ‘yancin yara.

Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yancin yara, ana kallon wannan yarjejeniyar, a mtsayin mafi girma a cikin tarihi.

Kazalika ma, yarjejeniyar, ta tabbatar da ci gaba da dorewar rayuwar yara, bunkasa rayuwarsu, ba su kariya da kuma shiga a dama da su kan abuwan da suka shafi ci gabansu.

Sai dai, abin takaicin shi ne, a namu ra’ayin, rashin wanzar da irin wadannan ‘yancin na yaran, hakan ne ya sanya ake sa yaran yin aikin wahala, sace su da kuma yin watsi da su.

A nan, muna kiran gaggawa da gwamnati ta kara kaimi wajen kara jaddada dokar bai wa yaran kariya da kuma magance taskun da suke ci gaba da fuskanta na matsin rayuwa, da suke ci gaba da fuskanta.

Wannan jaridar bisa la’akarin da ta yi a 2024, jihohin kasar nan 24 ne kacal, daga cikin jihohi  36 na kasar ne suka rungumi tsarin dokar bai wa yara kariya.

Sauran jihohin da ba su rungumi wannan dokar ba sun hada da; Gombe da kuma Bauchi.

Mun damu matuka, kan yadda ake kara samun yawan yaran da ba a kulawa da rayuwarsu a kasar.

Babbar Darakta ta Asusun UNICEF Catherine Russel, ta yi ikirarin cewa, hukuncin da shugabannin duniya suka yanke a yau ko kuma suka gaza dauka, zai fayyace wacce irin rayuwa ce, yara a duniya, za su iya tsintar kansu a ciki.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Ra'ayinnmu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Waiwaye a Kan Wasu Labarai Mafi Muhimmanci Game Da Mashigin Tekun Yankin Taiwan a 2024 Da CMG Ya Gabatar

Next Post

Abuubuwan Da Suka Fi Daukar Hankalin ‘Yan Nijeriya A 2024

Related

Daurarru
Ra'ayinmu

Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan

1 week ago
NCC
Ra'ayinmu

Bukatar Kawo Karshen Karin Kudin Kiran Waya Da Na Data

2 months ago
Ra'ayinmu

Gangamin Yaki Da Cutar Kuturta A Nijeriya

3 months ago
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Ra'ayinmu

Kisan Jami’an ‘Yansanda 229 A Cikin Wata 22 Babbar Musiba Ce Ga Kasa

5 months ago
Matasa 5 Cikin Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Sun yanke Jiki Sun Faɗi A Kotu
Ra'ayinmu

Batun Tuhumar Ƙananan Yara Da Laifin Shirya Juyin Mulki

6 months ago
Barazanar Da ‘Yan Jarida Ke Fuskanta A Bakin Aiki
Ra'ayinmu

Barazanar Da ‘Yan Jarida Ke Fuskanta A Bakin Aiki

6 months ago
Next Post
Abuubuwan Da Suka Fi Daukar Hankalin ‘Yan Nijeriya A 2024

Abuubuwan Da Suka Fi Daukar Hankalin ‘Yan Nijeriya A 2024

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

May 10, 2025
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

May 10, 2025
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

May 10, 2025

Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ba Dalibai 164 Tallafin Karatu

May 10, 2025
Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

May 10, 2025
Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

Sin Ta Nemi Indiya Da Pakistan Su Muhimmanta Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

May 10, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow

May 10, 2025
Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu

May 10, 2025
Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

May 10, 2025
Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.