Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ƙaryata jita-jitar da ake yi cewa ya koma jam’iyyar adawa ta PDP ko wata jam’iyya, yana mai bayyana labarin a matsayin ƙarya. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, El-Rufai ya ce ya miƙa batun ga lauyoyinsa don ɗaukar matakin doka.
Wani hadiminsa ya bayyana wa manema labarai cewa jita-jitar ba gaskiya ba ce, yana mai cewa aikin masu neman rura wutar rikici ne kawai. Rahoton ya kara cewa tsohon gwamnan bai karɓi katin zama memba na PDP daga Unguwar Sarki a Kaduna ba, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.
- Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Yarinya Ɗaya da Mutum 2 A Kaduna
- Mataimakiya Kan Harkokin Siyasa Ga Gwamnan Kaduna, Rachael Averik, Ta Tsallake Rijiya Da Baya
Wasu rahotanni na kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa El-Rufai ya koma PDP domin takarar shugabancin ƙasa a 2027, amma tsohon gwamnan ya nemi jama’a su yi watsi da wannan rahoto, yana mai tabbatar da cewa babu gaskiya a ciki.