Gwamnatin Tarayya ta musanta rahoton da jaridar Daily Trust ta buga a ranar 21 ga watan Janairu, wanda ya yi iƙirarin cewa ma’aikatar ayyuka ta bayar da kwangilar gyaran hanyar Abuja zuwa Kano ga wani kamfani mai suna Infoquest Nigeria Ltd, wanda aka ce ba ya aiki.
A wani taron manema labarai a Abuja, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana rahoton a matsayin abin takaici da ka iya tayar da hankalin jama’a.
- An Watsa Shirin Fadakarwa Na Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Masar
- Tsaftar Muhalli: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci Domin Tsaftace Jihar Zamfara
Ya ce rahoton ya yi zargin cewa an bai wa kamfanin Infoquest Nigeria Ltd kwangilar Naira biliyan 252.89 domin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna da Zariya zuwa Kano.
Ministan ya jaddada cewa ba gaskiya ba ne, domin kamfanin da ke da alaƙar kwangilar shi ne Infiouest International Limited, wanda ke aiki yadda ya kamata kuma ya cika duka sharuɗan da doka ta tanada.
Ya buƙaci jaridar Daily Trust da ta nemi afuwar jama’a da ma’aikatar ayyuka ta hanyar wallafawa aƙalla a jaridu biyar na ƙasar.
A wannan wata na Janairu ne gwamnatin tarayya ta sake bayar da kwangilar aikin hanyar Abuja zuwa Kano bayan ta ƙwace aikin daga kamfanin da aka bai wa tun farko.
Ministan yaÉ—a labarai ya bayyana cewa aikin zai kammala cikin wata 14.
Babbar hanyar Abuja zuwa Kano tana daga cikin manyan ayyukan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayar, amma ba a kammala ba har zuwa yanzu.
Wannan ya janyo suka da tattaunawa masu yawa a majalisar dokoki da sauran wurare.