An sallami tauraron Bollywood, Saif Ali Khan, daga asibitin Lilavati da ke birnin Mumbai kwanaki biyar bayan wani mutum ya kai masa hari da wuka a gidansa, in ji kamfanin dillancin labarai na PTI.
Rahotanni sun bayyana cewa, matarsa, Kareena Kapoor, ta je asibitin don ɗaukar shi.
- An Watsa Shirin Fadakarwa Na Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Masar
- Tsaftar Muhalli: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci Domin Tsaftace Jihar Zamfara
Da safiyar ranar Alhamis, wani mutum ya shiga gidan Saif da ke Bandra inda ya caka masa wuka a wurare daban-daban, lamarin da ya sa ya samu munanan raunuka.
Saif ya ji rauni a wurare shida, ciki har da ƙashin bayansa da wuyansa.
Likitoci sun ce sun cire wuka mai tsawon inci biyu da rabi daga ƙashin bayansa.
Ƴansandan Mumbai sun kama wanda ake zargin, mai suna Mohammad Shariful Islam Shahzad, wanda ake tunanin ya shiga gidan da nufin yin sata.
Mataimakin kwamishinan ƴansanda na shiyyar Mumbai-9, Dixit Gedam, ya ce Shahzad mai kimanin shekara 30 ne kuma mazaunin yankin West Bengal.
An kama shi a Hiramandi Labor Camp da ke Thane, kuma tuni aka fara bincike kan lamarin.