Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya gana da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, a yau Litinin.
Atiku, wanda ya isa gidan Obasanjo da ke cikin harabar Ɗakin Karatu da Tarihi na Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (OOPL), da misalin karfe 12:37 na rana, ya samu rakiyar tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da na Jihar Kuros Riba, Sanata Liyel Imoke, tare da wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewa.
- “Mun Yi Nasarar Yakar ‘Yan Bindiga”, Gwamna Lawal Ya Shaida Wa Bankin Duniya
- ‘Yan Fashi Da Makami Sun Kashe Limamin Coci A Gombe
Bayan isarsu, Atiku tare da tawagarsa sun samu tarba daga dattijon ƙasa, Otunba Oyewole Fasawe, a gidan Obasanjon, kana suka shiga kai tsaye domin ganawar sirri da tsohon Shugaban ƙasar, wanda ke jiran zuwansu.
Duk da cewa, cikakken bayani kan wannan ziyara bai fito fili ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, LEADERSHIP ta tattaro cewa, ganawar ba za ta rasa nasaba da burin Atiku na tsayawa takarar shugabancin Nijeriya ba a zaben 2027 mai zuwa.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, manyan ‘yan siyasar ba su kammala ganawar ba.