Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Neja a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Umar Muhammad Bago ya nesanta kan sa da alakanta shi da ‘yan daba da ke garin Minna.
Dan takarar ya bayyana cewa wajibi ne gwamnatin Jiha Neja ta dauki matakin ba sani ba sabo ga duk wanda aka samu da hannu wajen gudanar da ayyukan dabanci yake kokarin zama ruwan dare a Minna, domin wannan aikin ba zai kawo zaman lafiya da ci gaba a jihar ba.
- Nasarori Da Matsalolin Da NAHCON Ke Samu Wajen Gudanar Da Aikin Hajji
- Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa
Hon. Bago ya bayyana hakan a wani taron wayar da kai na illar ayyukan daba da sara suka da gwamnatin jiha ta shirya a babban dakin taro na Legbo Kutigi da ke Minna karshen makon nan da ya gabata.
Ya ci gaba da cewa bai yiwuwa matasa su rika daukar makamai suna far wa jama’a suna sacesace da illata lafiyar al’umma, sannan su rika samun daurin gindin wasu manya kuma a zura ido ana kallonsu.
Gwamnatin jiha dai ta ce tana bakin kokarinta wajen kawo karshen lamarin, inda mafi yawan lokuta idan matasan sun fito jami’an tsaro da suka kunshi ‘yan sanda da ‘yan sa-kai suke yunkurin tarwatsu wani lokaci har da kame wasu daga cikinsu, wanda bayan kwana biyu kuma sai a sako su saboda sanya bakin wasu manyan ‘yan siyasa a jihar.
Jama’a da dama sun zargi wasu gurbatattun lauyoyi da ‘yan siyasa da ke sanya baki wajen sake ‘yan dabar da aka kama da sunan ‘yancin Dan’adam