Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta taba maimaita yakin basassa irin na shekarar 1967, wanda ya girgiza kafuwar kasar nan.
Gwamna el-Rufai ya yi wannan gargadi ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron matasa masu bautar kasa (NYSC), kar su yarda a yi amfani da su wajen yin magudin zabe a 2023.
- Nasarori Da Matsalolin Da NAHCON Ke Samu Wajen Gudanar Da Aikin Hajji
- Gwamna Wike Ya Karyata Cire Tutocin PDP Daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas
el-rufai ya bayar da wannan shawarace a Kaduna a ranar Talata lokacin wajen taron fadakar da matasa ‘yan bautan kasa kasha na biyu na shekarar 2022.
Gwamnan wanda ya sami wakilcin mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Balarabe, ya ce yakin basasa ya yi matukar illata Nijeriya wanda ba a fatan ya kara faruwa a cikin kasar nan.
“Ya kamata matasa masu bautan kasa su sani cewa an samar da NYSC ne bayan yakin basasa da ya tarwatsa duk wani harkokin Nijeriya. Yakin ya daidaita kasar nan wanda ba a fatan ya kara faru a nan gaba.
“Domin haka, dole matasan Nijeriya su nesanta kansu da duk wani rikici da zai iya haddasa yaki a Nijeriya. Dole ne mu guji maimaita abubuwan da za su iya ruguza kasarmu ta gado. Ya kamata matasan Nijeriya su ki amincewa da bukatar masu son yaki a Nijeriya.
“Domin haka, ina kira da matasa masu bautar kasa su gudanar da abubuwan da suka dace wajen gina kasar nan. Babban makasudin da ya sa aka karkiri NYSC shi ne, inganta hadin kan Nijeriya gaba daya,” in ji el-Rufai.
Gwamna el-Rufai ya kara da cewa a matsayinsu na wakilan matasan Nijeriya su guji amsar cin hanci da rasawa lokacin zabe, domin hakan yana tarwatsa ci gaban kasar nan.