Tattalin arzikin cikin gida na Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba a zangon na hudu na shekarar 2024, inda ya samu havakuwa da kaso 3.84 cikin 100 da ya kai har naira tiriliyan 22.61.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya misalta wannan ci gaban da aka samu da ingantuwar kwazon vangaren da ba na mai ba, musamman sashin kudi da na inshora, sadarwa, noma, sufuri da adana.
- Za Mu Ƙalubalanci Ƙarin Kuɗin Kira Da Data A Kotu – NATCOMS
- Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
A cewar rahoton tattalin arzikin CBN na 2024, dukkanin vangarorin harkokin tattalin arziki sun samu tagomashi mai kyau na ci gaba amma ban da sashin wutar lantarki, gas, wadanda suka samu koma-baya da kaso 5.05 cikin 100.
An samu koma-baya a wannan vangaren ne sakamakon karin kudin wuta, da ci gaba da aikin gyaran layukan wuta da ake yi tare da karuwar sauyi a kokarin da ake yi na nemo hanyoyin rungumar makamashi.
Sashin vangaren mai ya samu dan kankanin ci gaba da kaso 1.48 cikin 100 a matakin shekara-shekara idan aka kwatanta da ci gaban da aka samu a vangaren da ba na mai ba wato ci gaba da kaso da 3.96 da sashin ya samar.
Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024.
Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana zuwa 1.43 ya taimaka wajen sanya sashin mai a matakin ci gaba na dan kadan a maimakon yin kasa sosai.
A gabaki-daya, sashin mai ya taimaka da kaso 00.7 cikin 100 na ci gaban tattalin arziki cikin gida (GDP) a tsawon wannan lokacin.
“Vangaren da ba na mai ba wanda ya samu tagomashi, ya samu saurin havaka da kaso 3.69 idan aka kwatanta da na zango na uku na 2024.
“Kuma wannan vangaren a gabaki-daya ya taimaka da kaso 3.77 na dukkanin ci gaban tattalin arziki, inda ya kasance sashin farko da ya jagoranci hadadar tattalin arzikin Nijeriya.
“Muhimman vangarorin da suka taka rawa wajen samun wannan ci gaba sun hada da sashin hada-hadar kudade da na inshora, vangaren sadarwa, sufuri, adana, amfanin gona da kuma vangaren kasuwanci.
“Vangaren kudade da inshora, musamman, sun samu ci gaba mai yawa saboda havaka fasahar kudi, ingantacciyar hanyar shiga banki, da karin zuba jari a kasuwanni,” in ji rahoton CBN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp