• English
  • Business News
Friday, August 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi

by Khalid Idris Doya
4 months ago
in Rahotonni
0
Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Nijeriya (NULGE), Alhaji Haruna Kankara, ya shaida cewar kusan jihohi 20 ba su aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashi na naira dubu 70 ga ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare ba.

Jihohin sun kunshi Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Kurus Ribas, Babban Birnin Tarayyar Abuja, Borno da wasu jihohi 11.

  • Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
  • Sin Ta Bayyana Wani Shiri Na Bunkasa Kiwon Lafiya

Shugaban na NULGE ya shaida hakan ne a lokacin da ke amsa tambayoyin ‘yan jarida kan batun mafi karanci albashi.

Bayan sanya hannu kan dokar sabon tsarin mafi karancin albashi ta 2024, jihohi da dama ne suka fara aiwata da dokar.

Jihohin sun kunshi Lagos, Ribas, Bayelsa, Neja, Inugu, Akwa Ibom, Abiya, Adamawa, Anambra, Jigawa, Gombe, Ogun, Kebbi, Ondo, Kogi da wasu.

Labarai Masu Nasaba

Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago.

Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.

Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba.

“Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun bar ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare, amma mun ci gaba da hada kai da rokon su da su yi wa wadannan ma’aikata abun da ya kamata.

“Wasu daga cikinsu sun yi alkawari amma sun kasa cikawa. Muna fatan nan ba da jimawa ba za a warware wadannan damuwowin,” in ji shi.

Dangane da aiwatar da dokar cin kashin kan kananan hukumomi kuwa, shugaban NULGE ya yi bayanin cewa har zuwa yanzu Babban Bankin Nijeriya bai tuntubi kananan hukumomi kan bude asusun bankuna ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: GwamnoniMafi Karancin Albashi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa

Next Post

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci

Related

Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa
Rahotonni

Dambarwar 2027 Da Kalubalen Da Ke Gaban Jam’iyyun Siyasa

6 days ago
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya
Rahotonni

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

1 week ago
Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda
Rahotonni

Tinubu Ya Yi Wa Arewa Kokari Fiye Da Duk Wani Shugaba A Tarihin Nijeriya -Kwamared Dauda

1 week ago
Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Rahotonni

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

4 weeks ago
Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
Rahotonni

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

4 weeks ago
Fyade
Rahotonni

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

1 month ago
Next Post
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (2): Kyawawan Dabi'u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama

August 22, 2025
UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya

August 22, 2025
Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

August 22, 2025
Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

Ɓarayin Waya Sun Hallaka Ɗalibin ATAP A Bauchi

August 22, 2025
JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa

August 22, 2025
Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

August 22, 2025
Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

Raguwar Hauhawar Farashi: ‘Yan Nijeriya Da ‘Yan Kasuwa Ba Su Ga Saukin A Zahirance Ba

August 22, 2025
Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

Kamfanin Novo Nordisk Na Denmark Zai Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar Sin A Bana

August 22, 2025
Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

Xi Jinping Zai Halarci Taron Kolin SCO Na 2025

August 22, 2025
Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City

Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City

August 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.