Mista Yakubu Lawal, Kwamishinan yada labarai da al’adu na Jihar Nasarawa da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi ya kubuta.
DSP Ramhan Nansel, kakakin ‘yan sandan jihar ne, ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), hakan a ranar Juma’a a garin Lafiya.
- Zan Tsamo Nijeriya Daga Matsalar Rashin Wutar Lantarki – Atiku
- Sin Ta Zama Daya Daga Cikin Kasashen Dake Sahun Gaba A Kirkire-Kirkire
NAN ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinan ne a gidansa da ke karamar hukumar Nassarawa-Eggon a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 9:45 na dare.
Kakakin, ya ce Kwamishinan ya kubuta ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Juma’a kuma tuni aka sada shi da iyalansa.
Ya ce an kuma kai wanda ya ji rauni zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.
Kakakin ‘yan sandan ya ce ba a kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da shi ba, amma ya ce ‘yan sandan ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun kama wadanda suka aikata laifin.
Sai dai Nansel, ya ce rundunar ‘yan sandan ba ta da masaniya ko an biya wani kudin fansa kafin a sako kwamishinan.
Ya bayyana cewa an saki kwamishinan ne saboda ci gaba da matsin lamba daga hadaddiyar tawagar jami’an tsaro ta yi.