Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke rangadi a wata masana’anta mai aiki da fasahar zamani dake lardin Henan na kasar a jiya, ya ce yadda kasar Sin ta nace ga kokarin raya bangaren masana’antu, ya sauya kasar, daga wadda ke bukatar shigar da sabulu daga ketare, zuwa wadda ta mallaki dukkan nau’o’in masana’antu masu inganci. Ya ce, “Mun bi hanyar da ta dace.”
Hakika yanzu ko masu takara da Sin ma, sun yarda da ci gaban masana’antun kasar. Misali, Kyle Chan, mai nazarin manufofin Sin a jami’ar Princeton ta kasar Amurka, ya rubuta wani bayani, wanda jaridar New York Times ta wallafa a kwanan baya, inda ya ce kasar Sin tana kan gaba a duniya a dimbin fannonin masana’antu, kana yana sa ran ganin karfin masana’antun kasar ya kai kaso 45% na dukkan masana’antun duniya, zuwa shekarar 2030.
- An Kama Mata Da Mahaifiyar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ado Aliero A Saudiyya
- ‘Yansanda Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Fashi, Sun Kama Wasu 7 A Abuja
Sai dai ta yaya kasar Sin ta cimma wannan nasara? A ganin mista Kyle, tsarin gwamnatin Sin na jagorantar aikin raya masana’antu ya taka muhimmiyar rawa, inda ya ba kasar Sin damar daidaita manufofi, da dora muhimmanci kan fannin masana’antu a kai a kai, ta yadda za ta iya cimma nasarar raya dimbin bangarori masu alaka da sabbin fasahohi na zamani.
Ganin nasarar da Sin ta samu ya sa mista Kyale damuwa sosai, a matsayinsa na Ba’amurke. Ya ce kasar Sin za ta iya zarce kasarsa ta Amurka, a karfin tattalin arziki da ingantattun fasahohi, ta yadda za ta iya daidaita tsare-tsare masu nasaba da iko a duniya.
Maganar Kyale ya shaida gaskiyar ra’ayin mista Stephen Akanbi, mai sharhi da na kan ga bayanansa a shafin yanar gizo na Opinion Nigeria. Ya taba bayyanawa cikin wani sharhinsa cewa, Amurka ta kan nuna kiyayya ga kasar Sin, ta fakewa da batutuwan “kiyaye tsaron kasa, da daidaiton ciniki, da hakkin dan Adam”. Amma a hakika, kasar tana tsoron kasar Sin, saboda nasarar da ta samu ta nuna wata sabuwar hanyar raya kasa, wadda za ta iya maye gurbin dabarar da kasashen yamma suka tsaya a kai.
A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu. Ban da haka, matsayin musamman na dalar Amurka a fannin ciniki, da yadda ake sarrafa farashin kudin, sun tsananta yanayin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, da jefa kamfanonin kasar cikin mawuyacin hali.
Ta yaya za a iya daidaita matsalolin da ake fuskanta? Mista Akanbi ya ba da shawarar daina dogaro da kasashen yamma, da tabbatar da bangarorin tattalin arzikin kasa da za a ba muhimmanci, bisa ra’ayin kasar, kamar yadda kasar Sin ta yi a baya. Ya ce, abokan hulda da Najeriya take bukata, su ne wadanda za su iya taimaka mata raya masana’antu, da zama mai zaman kai ta fuskar tattalin arziki. Saboda haka, karfafa hulda da kasashen BRICS, musamman ma kasar Sin, za su sanya Najeriya kama hanyar zama kasa mai karfin masana’antu, da na cinikayya.
Ci gaban kasa tamkar tafiyar da wani mutum yake yi. Idan wata hanyar da ake bi ba ta kai mutum inda ya nufa ba, to, sai a canza zuwa wata da daban. Wannan dabara ce da ta nuna hikima da sanin ya kamata. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp