Cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta sami gagarumin ci gaba a fannoni da dama, zaman rayuwar jama’a ta kyautatu matuka.
Daga shekarar 2012 zuwa 2022, karfin tattalin arzikin kasar Sin ya kai wani sabon matsayi. A shekarar 2021, ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin ya kai Yuan triliyan 114, adadin da ya kai kashi 18 bisa dari na karfin tattalin arzikin duniya, wanda bai wuce kashi 11.4 bisa dari ba a shekarar 2012. Kana, matsakaicin ma’aunin GDPn kasar Sin ya kai dallar Amurka dubu 12.5, adadin da ya kai kusa da na kasashe masu ci gaba.
Cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 bisa dari ta fuskar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wadda ta kasance babbar kasar dake taimakawa karuwar tattalin arzikin duniya.
Haka kuma, cikin wadannan shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta warware babbar matsalar fama da kangin talauci, wadda ta damu jama’ar Sin cikin dubban shekaru da suka gabata. Mazauna kauyuka kimanin miliyan 98.99 sun fita daga kangin talauci.
Adadin kauyukan da suka sauya zuwa birane, ya daga daga 53.1% zuwa 64.7%. Mazauna kauyuka kimanin miliyan 180 sun kaura zuwa birane. Kuma a shekarar 2021, yawan kudin da kowane mutum ya kashe bayan an biya haraji ya kai yuan dubu 35, kwatankwacin dallar Amurka 5197.5, adadin da ya karu da 80%, idan aka kwatanta da na shekarar 2012. Kana, yawan mutanen da suka samu matsakaicin kudin shiga ya karu daga kashi 1 bisa 4 zuwa kashi 1 bisa 3.
A fannnin kirkire-kirkire kuma, daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2022, kasar Sin ta mai da kirkire-kirkire matsayin mataki mafi muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban kasa. Adadin jarin da aka zuba a fannin kirkire-kirkire bisa ma’aunin tattalin arziki na GDPn kasar ya karu daga 1.91% zuwa 2.44%. Kana, matsayin kasar Sin cikin kasashen duniya da suka fi mai da hankali kan harkokin kirkire-kirkire ya daga daga matsayi na 34 zuwa matsayin 12, kuma, Sin ta zama kasa daya tilo da ta samu saurin bunkasuwa babu kakkautawa a wannan fanni.
Na’urar binciken duniyar Mars ta “Tianwen”, da na’urar binciken duniyar Wata ta Chang’e, da kuma yadda kumbon Shenzhou-13 mai dauke da mutane ya yi nasarar haduwa da cibiyar tashar sararin samaniyar Sin ta Tianhe, sun nuna gaggarumin ci gaba da kasar Sin ta samu a fannin binciken sararin samaniya.
Haka kuma, fasahohin jiragen kasa masu saurin gaske, da tsarin samar da wutar lantarki da fasahar sadarwa, da sabuwar fasahar samar da wutar lantarki mai amfani da makamashin nukiliya, dukkansu suna kan gaba cikin kasashen duniya.
Bugu da kari, muhallin kasar Sin ya kyautatu matuka cikin wadannan sheakru 10, ra’ayin “Koguna masu tsabta da tsaunuka masu kyau, dukuya ne masu daraja” ya samu karbuwa sosai a zakutan jama’ar kasar Sin.
A halin yanzu, yawan makamashi na bola-jari da aka adana a kasar Sin ya kai sama da kilo Watt (kW) biliyan 1, kuma adadin wutar lantarki da aka samar ta karfin iska, da karfin ruwa, da hasken rana ya kasance kan gaba a fadin duniya.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, adadin makamashi masu tsabta da aka yi amfani da su bisa dukkan makamashin da aka yi amfani da su a kasar Sin, ya karu daga 14.5% zuwa 25.5%. Kuma, cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan itatuwan da aka shuka a cikin kasar Sin, ya kai kashi 1 bisa uku na dukkanin itatuwan da aka shuka a fadin duniya, lamarin da ya sa, adadin hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da kasar Sin take fitarwa ya ragu matuka.
Haka kuma, daga shekarar 2012 zuwa 2022, yawan kudin shiga na al’ummomin kasar Sin na ci gaba da karuwa, kuma, zaman rayuwar jama’a ya samu kyautatuwa sosai, shi ya sa, karfin yin sayayya na jama’ar kasar Sin ya karu matuka.
A shekarar 2021, darajar jimillar kayayyakin yau da kullum da aka sayar a cikin kasar Sin, ta kai yuan triliyan 44.1, kwatankwacin dallar Amurka kimanin tirliyan 6.58, adadin da ya ninka sau 1.1 idan aka kwatanta da na shekarar 2012, wato adadin ya karu da 8.8% a ko wace shekara. Kuma, yin sayayya ya kasance abu mafi muhimmanci ta fuskar inganta karuwar tattalin arzikin kasar Sin.
Mazauna sassan kasar Sin su kan je kantuna ko yawo a tituna bayan aiki domin nishadi, kuma, wuraren yin sayayya iri daban-daban sun kara ci gaban birane sosai.
Bugu da kari, sayar da kayayyaki ta yanar gizo, gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin ’yan kasuwa na kasar Sin da na kasashen waje ta yanar gizo, da kuma biyan kudade da wayar salula, da sauran sabbin fasahohi da tsare-tsare na ci gaba da fitowa.
Tsoffin Kamfanoni da masana’antu suna gaggauta yin kwaskwarima domin hadewa da fasahohin zamani da na sadarwa, ta yadda za su sayar da kayayyakinsu ta hanyoyi guda biyu, wato ta hanyar da aka saba, da kuma ta yanar gizo. Lamarin da ya kara bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, ya kuma kawo babban sauyi ga zaman rayuwar jama’a na yau da kullum.
Kuma, kamar yadda muka sani, batun lafiyar mata da kananan yara, shi ne muhimmin tushen tabbatar da lafiyar dukkanin al’umma. Babban mizanin lafiyar mata da kananan yara ya hada da yawan mata masu ciki dake mutuwa yayin haihuwa, da yawan yara ‘yan kasa da shekaru 5 da jarirai dake mutuwa. Cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan mata masu ciki dake mutuwa yayin haihuwa, na ci gaba raguwa, kuma, babban mizanin lafiyar mata da kananan yara yana ci gaba da bunkasuwa kamar yadda ake fata, wanda ya kasance a kan gaba a wannan fanni, cikin kasashen da suka fi samun kudin shiga, da kasashe masu samun matsakaicin kudin shiga a duk fadin duniya. Lamarin da ya sa, hukumar kiwon lafiyar duniya wato WHO ta sanya kasar Sin cikin “kasashe guda 10 dake kan gaba a fannin kiwon lafiyar mata da kananan yara”.
Bugu da kari, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta bullo da tsarin ilimin gaba da sakandare mafi girma a fadin duniya, yawan mutanen da suka shiga manyan makarantu domin koyon ilimi ya karu daga 30% a shekarar 2012 zuwa 57.8% a shekarar 2021. Lamarin da ya nuna cewa, ilimin gaba da sakandare yana ci gaba da bunkasa, ta yadda galibin al’ummomin kasar Sin za su sami damar shiga manyan makarantu domin yin karatu.
Yawan mutanen da suka kammala karatu a manyan makarantu a kasar Sin ya kai miliyan 240, kuma, matsakaicin lokacin koyon ilimi na sabbin ‘yan kwadago ya kai shekaru 13.8, shi ya sa, kwarewarsu wajen gudanar da ayyuka ta karu sosai. Hakan ya sa, ingancin zaman rayuwar jama’ar kasar Sin yake ci gaba da samun kyautatuwa yadda ya kamata.
Kuma, cikin wadannan shekaru da suka gabata, an ci gaba da kyautata hanyoyin koyarwa, da tsarin gudanar da ayyuka a manyan makarantu, da kuma inganta yanayin koyo a manyan makarantu, domin ba da goyon baya ga duniyarmu ta fuskar zakulo mutanen dake da kwarewa, da kuma kara karfin yin kirkire-kirkire.
Haka zalika kuma, daga shekarar 2012 zuwa 2022, bangaren zirga-zirga na kasar Sin ya bunkasa sosai, lamarin da ya inganta jin dadin zaman al’umma. Kuma, alkaluman aikin zirga-zirga na layukan dogo, da manyan hanyoyi, da jiragen ruwa da kuma na jiragen sama da dai sauransu, suna kan gaba a duniya cikin shekaru da dama da suka gabata, hakan ya sa, kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen dake da yawan zirga zirgan ababen hawa.
Bisa bayanin da aka fidda a shekarar 2021, a ko wace rana, akwai jiragen ruwa sama da dubu 69 da suke shiga da kuma fita daga tasoshin jiragen ruwa, yayin da jiragen sama kimanin dubu 26.8 suke tashi da sauka a filin jiragen sama. Kana, ko wace rana, ana jigilar sakwanni kimanin miliyan 300. A wasu lokuta kuma, a ko wace rana, akwai jiragen kasa masu jigilar fasinjoji fiye da dubu 10 da suke tashi, yayin da motoci sama da miliyan 60 ke kai komo a kan manyan hanyoyin mota a duk fadin kasar Sin.
Ana iya cewa, Sinawa sun cimma burin “zuwa wuraren da suke fata, da aika sakwanni zuwa ko ina”, bunkasuwar aikin zirga-zirga ta sa al’ummomin kasar Sin sun gamsu matuka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)