Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshan Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano (YUMSFUEK) ta yi kira da a cire Farfesa Ahmad Adamu daga muƙaminsa na Shugaban Kwamitin Gudanarwa na jami’ar, saboda rikicin muradun da ke tattare da riƙe mukamin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
A cikin wata takarda da aka aika wa Ministan Ilimi, malaman sun zargi Kwamitin da keta ƙa’idojin zaɓen sabon Shugaban Jami’ar da kuma ƙoƙarin ci gaba da riƙe Dr. Sadi Mohammed Sirajo a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar. Sun yi iƙirarin cewa an cire wakilan Majalisar Dattawa, da Majalisar Malamai da na ƙungiyar Tsoffin Ɗalibai daga tsarin zaɓen.
- Yansanda Sun Fara Tsananta Daukar Mataki Kan Yan Daba A Kano
- Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai
ASUU ta bayyana cewa “duk wannan wasan kwaikwayo ne na Kwamitin da ya ƙeta ƙa’idoji don tilasta wanda suke so a zaɓa.” Sun kuma zargi Farfesa Adamu da goyon bayan ABU fiye da YUMSFUEK, da sake aza wutar rarrabuwa a cikin jami’ar.
Haka kuma, sun zargi Dr. Sirajo da ci gaba da riƙe mukamin shugaban jami’ar bayan ya ƙare wa’adinsa na wata 4, da kuma hana wasu malamai ci gaba da samun horo. Sun yi gargaɗin cewa idan ba a yi wani abu ba, hakan zai haifar da rikici a jami’ar.
Har yanzu ba a samu wani bayani daga Kwamitin gudanarwa ko shugabannin jami’ar ba. Ƙungiyar ta buƙaci Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Jami’o’i ta ƙaa (NUC) da su sa baki da gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp