“Zan so in koma gida ba tare da bata lokaci ba, don in gabatar da dabarun ga abokanan aikina”. A watan Afrilun bana, tawagar wakilan jam’iyyar UDA mai mulki ta kasar Kenya ta kawo ziyara kasar Sin a karkashin jagorancin babban sakatarenta Mr. Hassan Omar, kuma dabarun jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na gudanar da harkokinta sun burge su matuka. A cewar Mr. Omar, kasar Sin tana da kwarewa da dabarun saukaka fatara da tabbatar da adalci ga al’umma, wadanda suke iya zama abin koyi ga Kenya a kokarinta na aiwatar da gyare-gyare ga tattalin arziki da zaman al’umma da kuma siyasa.
A ganin mambobin tawagar Kenya, idan ana son fahimtar dalilin ci gaban kasar Sin, dole ne a fara da fahimtar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tukuna, kuma wannan ra’ayi yana ta kara samun karbuwa a tsakanin karin ‘yan siyasa da kwararrun masana na kasashe daban daban. Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin jam’iyya ce mai mulki a kasar, wadda aka kafa ta a shekarar 1921, kuma kawo yanzu shekarunta sun kai 104. Me ya sa jam’iyyar mai tsawon tarihi na sama da shekaru 100 har yanzu take dorewa a kan mulki? A ganina, babban dalili shi ne yadda jam’iyyar take daukar jama’a a matsayin tushen ayyukan da take sanyawa a gaba. A shekaru 80 da suka wuce, an taba yi wa tsohon jagoran jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin marigayi Mao Zedong tambaya cewa, ta yaya jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin zata iya dorewa? Ya amsa da cewa, “A bar jama’a su sa ido a kan aikin gwamnati”. Sai kuma da muka shiga sabon zamani, jam’iyyar ta gano sabuwar mafita, wato a dinga yi wa jam’iyyar kwaskwarima. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, “Kasa ita ce jama’a, kuma jama’a su ne kasa. Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci jama’a su kafa kasarsu da kiyaye ta, domin kiyaye imanin jama’a a kan ta.” Lallai bauta wa jama’a bisa iya kokarinta, shi yake samar wa jam’iyyar kwarin gwiwa da niyyar yi wa kanta kwaskwarima, haka kuma shi ne ainihin dalilin da ya sa take samun goyon baya daga jama’a.
- David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
- Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Kwana 60 Da Hamas – Trump
“Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana samun farin jini wurin jama’a, wannan kuma shi ne sirrin nasarorin da ta samu. Manufar gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya da ta gabatar ma tana shafar jama’a. Aminaina Sinawa su kan ce ‘kada mu manta da ainihin abin da muke neman cimmawa’, to, a ganina wannan shi ne abin da ake neman cimmawa”, in ji Jose Julio Gomez Beato, jakadan kasar Dominica a kasar Sin. Abin hakan yake, tun farkon kafuwarta, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta mai da samar wa al’umma alheri da kuma farfado da al’ummar Sinawa a matsayin ainihin abin da take neman cimmawa. Sai dai ba kamar jam’iyyun siyasa na wasu kasashe da su kan jaddada sanya kasashensu a gaba da kome ba, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a nata bangare tana kokarin amfanar al’ummar kasar, tana kuma kokartawa don tabbatar da ganin ci gaban dan Adam baki daya, wannan kuma shi ne dalilin da ya sa ta gabatar da manufarta ta “gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya”.
Alkaluman da aka samar a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata sun nuna cewa, kawo karshen bara, yawan ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya zarce miliyan 100, kuma yawan wadanda suka mika rokonsu na zama ‘ya‘yan jam’iyyar ya wuce miliyan 20, alkaluman da kuma suka shaida jam’iyyar na matukar samun karbuwa a tsakanin al’ummar kasar.
Tun bayan kafuwarta shekaru 104 da suka gabata, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci jama’ar kasar wajen samun nasarar juyin juya hali a kasar, daga nan kuma, ta jagoranci jama’ar kasar wajen tabbatar da saurin bunkasar tattalin arziki da al’umma mai zaman lumana a kasar, nasarorin da suka kasance na a zo a gani a duniya. Sabo da jama’a take kokartawa, kuma ta dogara da jama’a wajen cimma nasara.
‘Yan tawagar jam’iyyar UDA ta kasar Kenya da suka kawo ziyara kasar Sin sun kwatanta jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da bishiyar kuka, suna cewa, “Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tamkar bishiyar kuka ce, wadda ke da ingantattun saiwoyi da ma babban karfi na warkar da kanta, tana ta fid da furanni da ‘ya’ya ba tare da tsayawa ba” “bishiyoyin kuka suna da tsawon rai na sama da shekaru dubu”. Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana cikin karfinta, kuma za ta ci gaba da kokartawa domin bauta wa jama’a, tare da dogara da jama’a don cimma karin nasarori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp