An kusa fara Gasar Cin Kofin Afirka ta Mata (WAFCON), inda Morocco za ta karbi bakunci karo na biyu a jere. Za a fara buga wasannin ne daga ranar Asabar 5 ga watan Yuli, inda mai masaukin baki, Morocco za ta fafata da Zambiya a filin wasa na Olympic a birnin Rabat. Kasar da ta lashe kofin karo tara a tarihi, Nijeriya tana cikin wasannin, wadda za ta fara kece raini da Tunisia a rukuni na biyu a makon farko sai kuma rike da kofin, Afirka ta Kudu za ta kara da Ghana a wasan farko a rukuni na uku ranar Litinin 7 ga Yuli.
An raba tawagar 12 zuwa rukuni uku, inda kowane rukuni ke dauke da tawaga hudu. Mai masaukin baki Morocco tana da jan aiki a gabanta a rukunin farko, an kuma hada ta da Zambiya, wadda ta doke a wasannin neman shiga Olympic 2024. Haka kuma Morocco za ta fuskanci Senegal da Jamhuriyar Congo, inda biyu ne za su kai zagaye na biyu a gasar.
- Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali
- Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC
Tawagar Nijeriya na fatan sake lashe kofin, wanda rabonta da shi tun 2018, kuma ita ce kan gaba wajen iya kwallo a Afirka sannan ta 36 a duniya. Tawagar Nijeriya ta Super Falcons za ta kece raini a rukuni na biyu da ya kunshi Tunisia da Algeria da kuma Botswana.
Rukuni na uku kuwa ya hada da mai rike da kofin, Afirka ta Kudu, wadda za ta fara fuskantar Ghana, sai kuma Mali, wadanda za su yi wasannin a karo tun bayan 2018 da kuma Tanzania, wadda za ta buga gasar a karo na
biyu tun bayan 2010. Duk kungiya biyu da ta hada maki da yawa za ta kai zagayen gaba a kowanne rukuni da kuma biyu da suka sami maki mai yawa, amma suka kara a mataki na uku a cikin rukuni.
Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo
Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana.
Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania.
Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli. Sannan a lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT. Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli.
Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su, ba bu su daga cikin wadanda za su karbi bakuncin gasar bana. Kasar dake Arewacin Afirka na ci gaba da yin tsare-tsare da gyare-gyare, wadda za ta karbi bakuncin wasan cin kofin Afirka na maza da yin hadakar gasar cin kofin duniya da za a buga a 2030.
Za A Yi Amfani Da Filayen Wasa Shida A Birane Biyar Har Da Biyu A
Casablanca:
Olympic Stadium a Birnin Rabat (Mai cin ‘yan kallo 21,000)
El Bachir Stadium a Birnin Mohammedia (Mai cin ‘yan kallo 15,000)
Larbi Zaouli Stadium a Birnin Casablanca (Mai cin ‘yan kallo 30,000)
Pere Jego Stadium a Birnin Casablanca (Mai cin ‘yan kallo 10,000)
Honneur Stadium a Birnin Oujda (Mai cin ‘yan kallo 19,800)
Berkane Stadium a Birnin Berkane (Mai cin ‘yan kallo 15,000
Daga kasashe 12 da za su buga gasar cin kofin Afirka a Morocco, NIjeriya ce da Afirka ta Kudu ta taba daukar kofin. Super Falcons za ta fafata a wasannin karkashin koci, Justin Maduguwu. Chiamaka Nnadozie daga NIjeriya ita ce ta lashe kyautar fitatciyar mai tsaron raga a Afirka karo biyu, yayin da Asisat Oshoala za ta buga wasannin da ta dunga yin fice a baya.
Mai horar wa Desiree Ellis za ta yi kokarin kare kofin da yake hannun Afirka ta kudu, wadda za ta buga karawar ba tare da Thembi Kgatlana, saboda wasu dalilai na kashin kai. Haka ‘yar wasan Afirka ta Kudu, Jermaine Seoposenwe tana taka rawar gani a Monterrey a Medico da Hilda Magaia, wadanda aka rabawa takalmin zinare a matakin kan gaba a cin kwallaye a WAFCON a 2022.
Morocco tana zuba hannun jari mai yawa a fannin kwallon kafa a ‘yan shekaru da yawa, amma har yanzu tawagarta ta mata ta kasa kwaikwayon ta maza da ta taba taka matakin farko a buga wasa a Afirka. Sai dai Atlas Lionesses tana da mai horar wa Jorge Bilda, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Sifaniya a 2023. Zambia ta kare a mataki na uku a gasar baya da aka yi, tana kuma tare da wadda ta yi fice a fannin buga
mata wasa a Afirka a shekara, Barbra Banda, wadda ba ta buga gasar 2022 ba.
Mai buga wasa a Orlando Pride tana kan ganiya, wadda take wasa tare da Racheal Kundananji, wadanda suna daga cikin ‘yan wasa hudun da aka saya mafi tsada a tarihi. Ita kuwa ‘yar kasar Swistzerland, Nora Hauptel za ta ja ragamar Ghana ne domin lashe gasar karon farko a tarihi.
Bayan Nijeriya da Afirka ta Kudu da suke da tarihin lashe gasar kofin Afirka, Ghana tana da kwarewar halartar wasannin da ta yi a 1998 da 2002 da kuma 2006.
Wasannin cikin rukuni
Asabar 5 ga watan Yuli
Rukunin farko: Morocco da Zambia – Ranar Lahadi 6 ga watan Yuli
Rukunin farko: Senegal da Ibory Coast, El Bachir Stadium, Mohammedia
(14:00)
Rukunin na biyu: Nijeriya da Tunisia, Larbi Zaouli Stadium, Casablanca (16:00)
Rukunin na biyu: Algeria bs Botswana, Pere Jego Stadium, Casablanca (19:00)
Ranar Litinin 7 ga watan Yuli
Rukunin na uku: Afirka ta Kudu da Ghana, Honneur Stadium, Oujda
(16:00)
Rukunin na uku: Mali da Tanzania, Berkane Stadium, Berkane (19:00)
Ranar Laraba 9 ga watan Yuli
Rukunin farko: Zambiya da Senegal, Mohammedia (16:00)
Rukunin farko: Jamhuriyar Congo da Morocco, Rabat (19:00)
Ranar Alhamis 10 ga watan Yuli
Rukunin na biyu: Botswana da Nijeriya, Larbi Zaouli Stadium, Casablanca (16:00)
Rukunin na biyu: Tunisia da Algeria, Pere Jego Stadium, Casablanca (19:00)
Ranar Juma’a 11 ga watan Yuli
Rukunin na uku: Ghana da Mali, Berkane (16:00)
Rukunin na uku: Tanzania da South Africa, Oujda (19:00)
Ranar Asabar 12 ga watan Yuli
Rukunin farko: Morocco da Senegal, Rabat (19:00)
Rukunin farko: Zambiya da Jamhuriyar Congo, Mohammedia (19:00)
Ranar Lahadi 13 ga watan Yuli
Rukunin na biyu: Nijeriya da Algeria, Larbi Zaouli Stadium, Casablanca (19:00)
Rukunin na biyu: Tunisia da Botswana, Pere Jego Stadium, Casablanca (19:00)
Ranar Litinin 14 ga watan Yuli
Rukunin na uku: Afirka ta Kudu da Mali, Oujda (19:00)
Rukunin na uku: Ghana da Tanzania, Berkane (19:00)
Zagayen kwata fainal a WAFCON 2024
Ranar Juma’a 18 ga watan Yuli
Kwata fainal na farko: Wadda ta yi ta daya a rukunin farko da ta farko a rukuni na uku ko wadda ta yi ta uku a rukuni na biyu, za su yi wasa a Rabat
Kwata fainal na biyu: Wadda ta yi ta farko a rukuni na biyu da wadda ta yi ta biyu a rukunin farko, za su kece raini a Larbi Zaouli Stadium a Casablanca.
Ranar Asabar 19 ga watan yuli
Kwata fainal na uku: Wadda ta yi ta farko a rukuni na uku da ta daya a rukunin farko ko wadda ta kare a mataki na uku a rukuni na biyu, za su kara a Oujda
Kwata fainal na hudu: Wadda ta yi ta biyu a rukuni na biyu da wadda ta kare a mataki na biyu a rukuni na uku, za su yi wasa a Berkane
Wasannin dab da karshe a WAFCON 2024
Wasan dab da karshe na farko: Wadda ta ci zagayen kwata fainal a wasan farko za ta fuskanci wadda ta yi nasara a zagayen kwata final karawa ta hudu, za su kara a birnin Rabat.
Wasan dab da karshe na biyu: Wadda ta lashe zagayen kwata fainal wasa na biyu da wadda ta yi nasara a karawar kwata fainal na uku, za su kece raini a Larbi Zaouli Stadium a Casablanca.
Wasan neman mataki na uku da na hudu
Ranar Juma’a 25 ga watan Yuli
Wadda ta yi rashin nasara a dab da karshen farko da wadda aka doke a zagayen dab da karshe wasa na biyu, za su fafata a Larbi Zaouli Stadium a birnin Casablanca.
Wasan karshe na WAFCON 2024
Ranar Asabar 26 ga watan Yuli
Wadda ta lashe wasan farko na dab da karshe da wadda ta yi nasara a dab
da karshe na biyu, inda za su fafata a Olympic Stadium a Birnin Rabat.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp