Mai martaba Sarkin Maroko, Mohammed VI, ya aike da saƙon ta’aziyya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da al’ummar Nijeriya bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a birnin Landan ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
A cikin saƙonsa daga birnin Rabat, Sarkin ya bayyana Buhari a matsayin “ɗan ƙasa na ƙwarai” ga Nijeriya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar ƙasa da raya tattalin arziki. Ya ce dangantakarsu ta jagoranci ci gaban haɗin gwuiwa tsakanin Nijeriya da Maroko, musamman ta fuskar ayyukan raya kasa da suka haifar da sabuwar zumunta tsakanin ƙasashen biyu.
- Aikin Bututun Gas Na Nijeriya – Morocco Na Ƙara Samun Ci Gaba
- Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko
Sarkin ya ce yana miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari da ɗaukacin ƴan Nijeriya, yana mai addu’ar Allah ya gafarta masa.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kwanaki bakwai na zaman makoki a faɗin ƙasa, tare da umarnin sauke tutar Nijeriya zuwa rabin sanda, yayin da ake shirin gudanar da jana’izar Buhari a mahaifarsa Daura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp