Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wasu ɗalibai biyu na Makarantar Kwalejin Sakandare ta Gwamnati da ke Bichi, biyo bayan wani hari da wasu ɗalibai suka kai musu a cikin harabar makarantar.
Ɗaliban da suka rasu, Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa, an ce an kai musu hari da wani abu mai kaifi da ake kira ‘Gwale-Gwale’, wanda wasu tsofaffin ɗalibai suka yi amfani da shi bayan da suka zargesu da aikata wani laifi da ba a bayyana ba, kuma suka ɗauki doka a hannunsu.
- VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano
- Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Buƙatu 10 A Gaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulkin Nijeriya
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar ranar Talata, 16 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr. Ali Haruna Makoɗa, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya da adalci don gano haƙiƙanin abin da ya faru.
Babban Sakataren wanda ya kai ziyara makarantar, ya shawarci ɗalibai da su guji ɗaukar doka a hannunsu. “Ya kamata ku riƙa kai korafe-korafenku ga hukumomin makaranta domin ɗaukar matakin da ya dace,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan da lamarin ya rutsa da su, tare da addu’ar Allah ya ba wa marigayyu Aljannatul Firdaus.”
Ƙin jin daɗin iyalan ya fito fili, inda Malam Ibrahim Yusuf Dungurawa, dangin marigayi Umar, ya bayyana yadda suka firgita da jin labarin mutuwar ɗansu, yana mai roƙon gwamnati da ta tabbatar da adalci. Haka zalika, Malam Idris Garba Tofawa, mahaifin marigayi Hamza, ya bayyana lamarin a matsayin ƙaddara daga Allah, amma ya bukaci hukuma ta ɗauki mataki cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp