Tawagar kwararru masu gudanar da bincike na Cibiyoyin bincike a kan tsirrai ta kasa daga Jihohin Gombe da Kano (NIHORT), sun isa gonakin da ake noman Kankana a kauyen Bara da ke Karamar Hukumar Kirfi ta Jihar Bauchi, domin gudanar da bincike a kan wannan cuta da ta afka wa Kankana.
A makwannin da suka gabata, mun ruwaito muku cewa; Mataimaki a Sashen Cibiyar ta Jihar Gombe, Nasiru Usman ya bayyana cewa; za su kai ziyara Kauyen Bara, don tantance bayanai a kan wadannan matsaloli da noman Kankana a kauyen ke fuskanta, wanda hakan ya tilasta wa wasu daga cikin manoman Kankanan a Karamar Hukumar Kirfi ta Jihar Bauchi, yin hijira zuwa Kasar Kamaru.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Damammakin Raya Kai Ga Matasan Kasashen Afirka
- Matsalolin Da Hukumar JAMB Ta Fuskanta A Jarrabawar Bana
A jawabinsa a yayin ziyarar, Dakta Idris Bala Gingiyu ya ce, tagawar ta ziyarci gonar ne, don duba matsalar tare da samun sauran bayanan cututtukan da suka harbi Kankanar da kuma samfurin maganin feshin da manomanta suka yi amfani da shi a kanta.
Bagauda, wanda ya fito daga Cibiyar reshen Jihar Kano ya bayyana cewa, da izinin Allah tare da kokarin da Cibiyar NIHORT take yi, zamu lalubo da mafita a kan wannan kalubale da monoman Kankana ke fuskanta.