Shugaban kwamitin binciken da ya samar da irin masara mai jure fari da kuma farmaki da hare-haren kwari, Farfesa Rabiu Adamu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ya tabbatar wa da manoman Nijeriya cewa, a ckin watan 6 (Yuni) na shekara mai zuwa 2024 za su fara shuka irin TELA maize kamar yadda aka shirya. Ya ce, sanannun kamfanonin sayar da iri a fadin Nijeriya ne za su jagoranci sayar wa da manoma irin masarar.
Farfesa Adamu ya kara bayyana cewa, a wata biyu masu zuwa za a mika wa gwmanati cikakken halin da binciken ke ciki tare da cika dukkan ka’idojin hukuma a kan irin na TELA daga nan kuma za a mika irin ga ‘yan kasuwa don manoma su ci gaba da amfana.
- Yaki Da Badala: Kamen Hisba Na Tayar Da Kura A Kano
- Yadda Taron Baje Kolin CIIE Karo Na 6 A Birnin Shanghai Ya Gudana Cikin Armashi
Farfesa Adamu ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a babban taron da ke gudana a kan harkar gona a halin yanzu a garin Nairobi ta kasar Kenya, ya kuma ce TELA maize zai samar da karin kashi 20 na abin da za a girba in aka kwatanta da sauran masara na yau da kulum.
“Mun yi kokari sosai, babu abin da zai dakatar da mu, muna a matakin karshe ne, muna kuma son ci gaba da bin dukkan ka’idojin da ake bukata ne. Daga karshen wata Disamba zuwa watan Janairu na shekara mai zuwa za mu cika dukkan ka’idojin da ake bukata, daga nan kuma a watan Yunin 2024 manoma za su fara shuka irin su kuma ci gaba da cin gajiyar amfanin shi a karon farko a Nijeriya.
“TELA maize’ yana jure farmakin kwari yana kuma jure wa fari, noma shi zai samar da karin yabanya mai yawa, muna fatan manoma za su fara amfani da irin a tsakanin watan Mayu da Yuni na shekarar 2024.
Farfesa Adamu ya kara da cewa, a kwai shirin hadin gwiwa da wasu kamfanoni masu zaman kansu don su taimaka wajen samar da karin irin don a tabbatar da wadatarsa a fadin tarayyar Nijeriya.