Watakila shugaban kasar Amurka Donald Trump yana son wasan kati, saboda yana yawan ambatonsa. Ya taba bayyana wa takwaransa na kasar Ukraine Vladimir Zelenski cewa, ” Ba ka da kati a hannunka, saboda haka ba za ka ci nasara ba. ” Kana a kwanan nan, shugaba Trump ya ce kungiyar kasashen Turai ta EU za ta “nuna sassauci” ga kasar Amurka, dangane da batun cinikayya, saboda Amurka ta rike “dukkan katunan da take bukata”.
Kasancewarsa shugaban wata babbar kasa mai karfi, Mista Trump na kallon kansa a matsayin “mai rike da dimbin katuna masu kyau”, wanda yake iya kalubalantar kasashen duniya. Saboda haka, kasar Amurka ta kaddamar da yakin haraji, inda ta sanar da karbar karin harajin fito kan kayayyakin wasu kasashe 76. Sa’an nan, matakin da Amurka ta dauka, ya sa kasar Sin mayar da martani.
- Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil
Bayan Sin da Amurka sun kakaba wa juna wasu matakai na karbar karin harajin fito, kasar Amurka ta fahimci zai yi wuya ta kai labari, don haka ta gayyaci kasar Sin su koma teburin shawarwari, inda kasashen biyu suka daddale yarjejeniyar rage harajin fito. A wajen “wasan kati” na wannan karo, kasar Sin ta ci nasara, in ji kafofin watsa labaru na kasar Amurka. Inda kamfanin dillacin labaru na Bloomberg na kasar Amurka ya ce, “Matakai masu karfi da kasar Sin ta mayar wa kasar Amurka sun yi amfani, inda suka sanya Amurka ja da baya, da bai wa Sin damar samun biyan bukata a harkar cinikayya.”
Ko da yake, ba za mu ce “wasan kati” da kasar Amurka ta kaddamar ya riga ya kai karshe ba, amma za mu iya samun wasu fasahohi, bisa nazari kan yadda kasar Sin da sauran kasashe suka yi cudanya da kasar Amurka.
Da farko, idan ana da kati a hannu, sai a dauki mataki ba tare da wata-wata ba.
Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba. Musamman ma ta la’akari da yadda kasar ba ta rasa “kati” a hannunta ba, inda karfin tattalin arzikinta, da manufar bude kofa da ta dauka, dukkansu suka kasance karfinta na tinkarar kalubale.
Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da ya kamata mu lura da shi, shi ne, yayin da muke fuskantar matsin lamba daga kasar Amurka, kar mu yi kasa a gwiwa, maimakon haka ya kamata mu yi kokarin hadin gwiwa da abokan hulda.
Bayan da kasar Amurka ta kaddamar da yakin haraji, kasar Japan ita ce kasa ta farko da ta tura wakili zuwa kasar Amurka, don rokon a yafe mata harajin da aka kara. Amma ba ta samu komai ba, ta tashi a fankan-fayau balle ma a batun harajin kwastam mai matukar tsanani. Ganin haka ya sa kasar Japan ita ma ta dauki “kati”, ta fara wasa da shi, inda kasar ta sanar da cewa ba za ta taba hakuri da manufar haraji ta kasar Amurka ba. Kana jaridar Labarun Tattalin Arziki Na Kasar Japan ta wallafa wani bayani mai taken “Matakan Kasar Amurka Za Su Haifar Da Tsarin Cinikin Duniya Da Bai Kunshi Kasar Amurka Ba”.
A hakika, ana kan hanyar samun wani tsarin cinikin duniya, da bai shafi kasar Amurka ba, ko kuma ba zai tasirantu da Amurka ba. Idan mun lura da ayyukan da dimbin kasashen nahiyoyin Asiya, da Afirka, da Latin Amurka suke yi, da sanarwoyin kasashen BRICS, da na kungiyar kasashen Afirka ta AU, to, za mu san cewa, kasashe masu tasowa suna kokarin karfafa hadin kansu a fannin tattalin arziki da cinikayya, da daidaita tsare-tsaren samar da kayayyaki, ta yadda za su samu sabbin damammakin raya kansu, yayin da ake fuskantar daidaituwar yanayin tattalin arzikin duniya.
Haka zalika, wata shawara mafi muhimmanci ita ce, a yi watsi da burin zama abokiyar kasar Amurka.
Saboda Amurka na kallon moriyar kanta a gaba da komai. Don haka, idan wata kasa tana son zama abokiyar huldar kasar Amurka, to, wata rana za ta ga yadda kasar Amurka ta mai da ita tamkar abokiyar gaba. Wannan dabarar kasar Amurka ta sa Ukraine rasa albarkatun kasarta, kana kasar Canada ta zama “jiha ta 51 ta kasar Amurka” a idon Amurka din. Yayin da kasashen Turai, ko da yake suke son taimakon kasar Amurka wajen dakile tattalin arzikin Sin, sai dai duk da haka, kasar Amurka na son ganin yadda kasashen Turai su nuna sassauci, da zama wani bangaren da kasar Amurka za ta iya kwatar dukiyoyinsa yadda ta ga dama. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp