Abbas Balarabe, ya yanke jiki ya fadi a lokacin da majalisar dattawa ke tantance shi a gaban kwamitin tantance ministoci.
Balarabe dai ya kammala karanta takaitaccen tarihinsa, yayin da majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa karfe 2 na rana, lokacin da lamarin ya faru.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya zabi Abbas a matsayin wanda zai maye gurbin El-Rufai daga jihar Kaduna a matsayin minista.
Idan ba a manta ba, majalisar dattawa ta ki tantance tsohon gwamnan Kaduna, kan rahoton tsaro da DSS suka bayar a kansa.
Rashin tantance El-Rufai ya bar baya da kura tare da haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Wasu na ganin tsohon gwamnan na da kwarewar da ya kamata ya zama daya daga cikin jerin ministocin gwamnatin Shugaba Tinubu duk da rahoton da aka bayyana a game da shi.
A gefe guda kuwa wasu na ganin tsohon gwamnan na Kaduna, ya yi wasu kalamai masu tsauri da suke da alaka da tsaro wanda ake ganin su ne dalilin da ya sanya aka ki aminta da shi.