Damuwa babbar cuta wadda ta shafi hankalin mutum tana kuma tafe da alamu uku wadanda suke nuna cewa lalle da akwai matsala, wadannan alamomin sun hada da mutum ya nuna damuwa,bakin- ciki,nuna bai damu da wasu al’amuran da suka faru a baya.Wadanda kuma ya ji dadinsu ba,ya kuma nuna gajiya cikin sauki.
Darektan kula da lafiya na Asibitin Mahaukata tarayya da ke Enugu Dokta Monday Igwe, ya bayyana sauran wasu alamun da suka hada da samun sauyi a dandano ko yayi sama ko kasa.Bacci ma ana samun canji na yin shi, kodai ya kasance ana samu kamar yadda ya dace ko kuma ba haka ba.
- NDLEA Ta Kwace Miyagun Kwayoyi Na Biliyan 450 A Wata 22 – Buba Marwa
- Babban Jami’in Kamfanin Max Air Ya Rasu
Hakanan ma nauyin mutum yana karuwa ko raguwa, akwai samun matsala wadda marasa lafiya da yawa, ke bayani da samun tabin hankali, mutum ya rika jin bai da gaskiya, ko ya rika ganin laifin kan shi ba gaira ba dalili.
Yace akwai yadda mutum zai rika ganin a kasa yake, bai da wata kima,ba wata tabbas, da ganin ba zai iya komai ba, babu tabbas kan abinda zai iya faruwa a gaba, ko ya rika jin zai rika tunanin yi ma kanshi illa, ko kokarin kashe kansa, duk alamu ne na cutar damuwa.
Da yake kwatance da hukumar lafiya ta duniya Igwe yace ko wacce shekara mutane milyan suna kashe kansu, inda ya kara da bayanin cewa kashi casa’in na abubuwan da suke sa kisan kai, na da alaka da cutar damuwa. “Wannan ya nuna kenan kowanne sakan arba’in ana samun mutum yan akashe kansa, a fadin duniya.Masu aikata wannan kuma laifin daga shekara 15 zuwa 45 ne.
Igwe ya ce yadda za a kula da cutar shi ne da zarar mutum yab fa ganin wadannan alamun sai yaga Likita ba tare da bata lokaci ba, sai a aje aga Likitan mahaukata, ko wanda yake kula da lafiyar iyali, domin bada shawarar data dace kan mataki na gaba.
“Sai dai kuma idan ana bukatar cikakkiyar kulawa akwai bukatar hada maganin da bada shawara
Da yake magana kan matakin da yafi dacewa ayi sai Likitan mahaukatan yace akwai abubuwa da suke kawo farinciki da suka hada da hakuri, samun cimma buri, su suka fi taimakawa wajen samun warkewa daga cutar damuwa.