Connect with us

WASANNI

Abin Da Ya Sa Aka Dakatar Da Kocin Nijeriya Tsawon Shekara Daya

Published

on

Kwamitin Da’a na Hukumar kwallon kafar kasar nan, NFF ya dakatar da babban kocin tawagar Super Eagles, Salisu Yusuf daga shiga harkokin wasannin kwallo har na tsawon shekara guda tare da cin sa tarar Dala dubu biyar.

Wannan na zuwa ne bayan wani faifen bidiyo ya nuna Kocin na karbar cin hancin Dala dubu daya daga hannun wani dan jarida da yayi bad da kama a matsayin wakilin dan wasa.

Dan jaridar ya gabatar da kansa a matsayin wakilin ‘yan wasa biyu da suka hada da Osas Okoro da Rabiu Ali, in da ya bada cin hancin don sanya ‘yan wasan cikin jerin sunayen masu wakiltar Nijeriya a gasar cin kofin zakarun kasashen Afrika ta 2018 a Morocco.

Koda yake Yusuf ya musanta aikata laifi, kuma yana da damar daukaka kara don kalubalantar wannan hukuncin da hukumar tayi masa.

A wani labarin daban,  jami’an tsaron sun cafke tsohon shugaban Hukumar kwallon kafar Benin, Anjorin Moucharafou kan zargin sace kayayyakin wasanni.

Majiyar shari’a ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, an tsare Moucharafou ne a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan batun satar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: