Al’ummar da ke yankin Mumuye a jihar Taraba, akasarinsu manoman doya ne kuma ta nan ne suke samun kudin biyan bukatunsu na yau da kullum.
A karamar hukumar Yorro da Zing an san al’ummar Mumuye wajen noman doya saboda haka suka kasance a kan gaba wajen noman doya a jihar.
Sai dai, babban kalubalen da suke fama da shi, shi ne na rashin hanya mai kyau da za su dinga yin safarar doyar da suka noma zuwa kasuwani, musamman kasuwannin da ke makwabtaka da jihar, inda ‘yan na-kama ke yin amfani da wannan damar wajen sayen doyar da suka hake da araha.
A dukkan kananan hukumomin biyu, babu wata shinfidaddiyar kwalata da gwamnatin jihar ta yi, musamman babbar hanyar da za ta sada sauran kauyukan da ke a yankunan.
Hanya daya da ta hada shalkwatar Pantisawa da ke a karamar hukumar Yorro da babbar hanyar Jalingo zuwa Yola, gwamnatin jihar Filato ce ta bayar da kwangilar ta, har yanzu ba a kammala ta ba.
Har ila yau, aikin babbar hanya daga Zing zuwa Monkin wanda aikin mazaba ne da mariganyiya Sanata Jummai Ai’sha Alhassan ta faro shi, sima an yi wasti da aikin.
Wata mace mai noman doya a yankin Nyadadi Gorko da ke a Yorro Zulai Muhammed ta koka ne a kan rashin hanya a daukacin yankin na Mumuye, inda ta kara da cewa, ba wani talafa da suke samu daga gun gwamnati kamar yadda gwamnatin ta ke yi wa manoman shinkafa da masara da kuma sauran manoman da ke noma sauran amfanain gona.
Zulai ta ci gaba da cerwa, noman doya abu ne mai wuyar gaske, domin aiki ne da ake shafe wata goma sha biyu ana gudanar da shi, da ya hada da, gyran gona, yin shuka da kuma yin girbi.
A cewarta, akasari ana fara gyaran gona ne a cikin watan Satumba, inda kuma ake fara yin shuka daga a watan Disamba, sannan kuma a hake ta a cikin watan Satumba, inda hakan ke nuna cewa, ana shafe shekara daya ne ana yin aikinta.
Zulai ta ce, manomamn doya na yin amfani da takin zamani kala biyu ne da wanda ke sa doyar saurin girma wato NPK da kuma wanda ke sa jijiyar doyar yin girma, inda ta kara da cewa, irin na doya da ake shuka wa yana tsada, inda hakan ke sanya wa sabon shiga cikin fannin bas a samu wata riba kirki.
Shi ma wani manomin na doya a yankin Haruna Hassan ya sanar da cewa, rashin yin kulawar da ta dace a fannin na jawo wa manomanta rashin samun riba mai yawa, wanda ya ce, akasarin manoman doya a yankunan har yanzu suna yin noman na ta hanyar gargakiya ganin cewa, ba a tanadar masu da kayan aiki na zamani ba.
Bugu da kari shi ma wani manomin doya a karamar hukumar Zing Bulus Shamaki ya bayyana cewa, akasarin maomnaon da ke Mumuye na sayar da wani kashi na doyar da suka noma ne domin su samarwa da kansu kuadaden shiga.
Ya sanar da cewa, akwai bukatar manoman na doya, musamman a yankuna da su hada kansu waje daya su kafa kungiya don yin magana da yawu daya a kan matsalolinsu da kuma yadda za su dinga samun rance don kara fadada sana’ar ta su.
Bugu da kari, shi ma wani manomin doya mai suna Yarima Isa Tafida anda ke da gona a Mumuye ya sanar da cewa, ya na nomanta da yawa.
A bisa wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, ana sayar manyan kwaryar doya a kan farashin naira 150,000, inda kuma ake sayar da kanana daga naira 45,000 zuwa naira 100,000.