Nijeriya da kasar Brazil, sun rattaba hannun yarjejeniyar kasuwaci data kai ta dalar biliyan 1.1
Aun rattaba hannun ne, a karkashin aikin GIP wanda zai tabbatar da an dauki matakan samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan.
Wannan na kunshe ne, a cikin sanarwar da mataiki na musamman a bangaren kayada labarai da samar da bayanai a ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya fitar a ranar Litinin .
Sanawar ta ce, aikin zai kuma taimaka wajen bunkasa aikin noma da kara karfafa vangaren zuba hannun jari na masana’antu, masu zaman kansu a kasar.
- Nijeriya Da Brazil Sun Cimma Yarjejeniyar Bunkasa Noman Zamani A Kasar Nan
- Nijeriya Da Brazil Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwanci Ta Dala Biliyan 1
An faro sanya hannun yarjejeniyar kashi na farko ta dala biliyan 1.1 a 2018, inda kuma kashi na biyu na yarjejeniyar da ta kai ta dala biliyan 4.3 da kuma ta dala biliyan 2.5 wadda ta kassance, ta JBS aka rattaba hannun ta, a Brazil, a yayin ziyarar aiki da shugaba Bola Tinubu ya kai kasar, a 2024, wacce kuma a akalla ta kai ta dala biliyan 8.
A jawabinsa a wajen ratabbta hannun yarjejeniyar Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, ya alakanta ratabbta hannun kashi na farko na GIP a matsayin ci gaba da kokarin da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kara samar da wadataccen abinci a kasar.
Rattaba hannun wadda ta gudana a Fadar Shugaban kasa da ke , Abuja, Shettima ya sanar da cewa, yarjejeniyar ta GIP za ta taimakwa waje kara havaka tattalin azikin kasar da kuma maidowa da masu son zuba hannun jari a tattalin arzikin kasar, kwarin guiwa.
Kazalika, Shettima ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar ta GIP, ta yi daidai da tsare-tsare da kuma shirye-shiyen Gwamnatin Shugaba kasa Bola Tinubu, musamman duba da cewa, za ta taimaka wajen hada kanannan manoma da sauran masu sayen kayan amfanin gona a kasar.
Shi kuwa Jakadan Brazil a Nijeriya, Mista Carlos Garcete ya ce, wannan yarjejeniyar abar alfahari ce, ga Brazil, inda ya ce, an shafe sama da shekaru bakwai ana tattaunawa a tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Brazil, bisa nufin karvar kudaden da suka kamata daga gun masana’antu masu zaman kansu da kuma bankunan da ke a yankuna, musamman domin a zuba kudaden a cikin wannan aikin, inda kudin akalla ya kai dala biliyan 1.1.
Ya kara da cewa, aikin zai kuma bayar da damar shigo da kayan aikin noma, zuwa cikin kasar nan, kamar irinsu Taraktocin noma da sauran kayan gyran kayan aikin noma.
Mista Carlos a madadin Gwamnatin Brazili, ya gaodewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kawo karshen tattaunawar ta zuba hannun jarin a kan wannan aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp