Abubakar Abba" />

Abinda Ya Sa Nijeriya Ta Ja Baya Wajen Noman Waken Soya

Noman Waken Soya

A shekaru da dama da suka gabata, kasar nan ta kasance kan gaba wajen noman waken soya.

Sai da, abin taiakaci, a yanzu ana fama da karancin na waken soya, a kasar, inda hakan, musamman ya jefa fannin kiwon kaji a kmkasar cikin Babbar matsala saboda karancinsa.

Har ila yau, lamarin ya haifar da tsadar kaji da kuma hauhawar farashin waken soya, inda kuma a cikin shekarar da ta gabata dai farashin waken soya ya nunka

Wani rahoto ya nuna cewa buhun waken soya mai nauyin kilogiram 100, wanda ake sayarwa naira 12,000 zuwa naira 13,000, ya rubanya zuwa naira 24,000.

A waa hira da Shugabar Katafariyar Gonar BD&S Farms Folake Aina wadda ke harkar kayan abincin kaji, ta bayyana gagarimar matsalar da masu harkokin kayan abincin kaji su ke fuskanta.

A cewarta, samun waken soya a yanzu babbar matsala ce. Idan ka ji ka saya da tsada a yau, to gobe ka koma za ka ji farashin ya tashi, inda ta kara da cewa, ka san kuma waken soya shi ne kashi 75 bisa 100 shi ake sarrafawa a yi abincin kaji da kuma masara ta biyo baya.

A makon da ya gabata naira 245 ake sayar da kilogiram daya ciki har da kudin dakon kaya, inda kuma kuma farashin ya karu zuwa 290.

Ta kuma bayyana cewa, waken soya na da karin sinadaran gina jiki, idan babu shi, to kaji ba za su samu isassshen abinci mai jina masu jiki ba, inda ta kara da cewa, ka san magana ce ake yi ta samar da nama da kwai mai inganci.

Har ila yau, an kuma ruwaito Babban Daraktan Kungiyar Masu Kiwon Kaji ta ta kasa Onallo Akpa, ya bayyana damuwar sa dangane da matsalar tsadar waken soya, inda ya kara da cewa, tan daya na waken soya wanda ake sayarwa naira 160,000 a cikin watan Oktoba, a yanzu ya kai naira 300,000 a cikin wannan wata.

Ya ci gaba da cewa, yawancin masu gidajen kaji sun kulle saboda matsalar kayan abinci. Inda ya bayyana cewa saboda yawancin masu kiwon kajin ko abincin kajin ma ba su iya saye.

A ceawrsa, wannan matsala ta na ci wa harkar kiwon kaji tuwo a kwarya sosai, saboda waken soya sa masara su ne kashi 80 bisa 100 na nau’o’in abincin kaji masu gina jiki.

Bugu da kari, an uma ruwaito wani mai sana’ar Olaseni Olasupo ya bayyana cewa, karancin kayan abincin ta kai masana’antun da ke samar masu da kayan abincin su na maido masu da kudade su.

A ceawrsa, rashin waken soya zai haifar da karancin sinadaran gina jiki a jikin kaji, inda ya kara da cewa hakan ya na sa ba a samu kosassun kajin da za su samar da kwayaye da yawa kuma idan. babu kwayaye da yawa kuwa, to kiwon kaji asara ce babu riba.

Har ila yau, shi kuwa, Shugaban Kungiyar Manoma Waken Soya na Kasa, Nafiu Abdu, ya ce ya zama dole gwamnatin tarayya ta taimaka wa manoma da sauri domin samar da abincin kaji musamman waken soya, ba sai an bari sai cikin watan Yuli ko Agusta ba, sannan wuri ya kure, an makara.

Exit mobile version