Fadar shugaban kasa ta zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi bisa shigo da wasu abubuwa guda biyu masu hatsari a cikin siyasar Nijeriya a zaben da ya gabata.
Mashawarcin shugaban kasa, Bayo Onanuga, shi ne ya zargi Peter Obi da shigo da addini da kabilanci cikin siyasar Nijeriya a lokacin zaben 2023.
- Mun Dukufa Magance Matsalolin Bangaren Lantarki, In Ji Minista
- Yadda Musulmi Ke Shirye-shiryen Bikin Karamar Sallah Cikin Tsadar Rayuwa
Mashawarcin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a wani shirin gidan rediyo tare da Seun Okinbaloye, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu za ta mayar da hankali kan abubuwan da ta sa a gaba na ci gaba ba damuwa da maganganun ‘yan adawa ba.
Onanuga Ya bayyana hakan ne domin mayar da martini ga Peter Obi bisa kalaman da ya yi cewa ya damu kwarai da yadda gwamnatin APC take ci gaba da kinkimo bashi a gida waje.
A dai cikin wannan makon ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnatin APC ke ci gaba da ciyo wa ‘yan Nijeriya bashi a shafinsa na twitter. “A sulusin farko na 2023, ana bin Nijeriya bashin naira tiriliyan 87.9, inda aka samu karin naira tiriliyan 10 a karshen shekarar 2023. Wannan babban abun takaici ne kuma ya kamata gwamnatin APC ta nemo hanyar warware lamura ba ta hanyar bashi ba,” in ji Obi.
A martanin nasa, Onanuga ya ci gaba da cewa gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ba ta damuwa ko mayar da hankali kan Peter Obi da magoya bayansa.
Mashawarcin ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da yin aiki tukuru ba tare da damuwa da zargin ‘yan adawa ba.
“A yanzu haka, mun mayar da hankali kan gudanar da harkokin gwamnati kuma ba mu son a karkatar da hankalinmu kan abin da gwamnati ta saka gaba a kai. A kowani lokaci muna cikin aiki ba mu ko kallon ‘yan adawa masu suka.
“Abin da na sani game da yakin neman zaben Peter Obi shi ne, a karon farko a tarihin siyasar Nijeriya mun sami dan takara da ya bijiro da tsattsauran ra’ayin kabilanci da addini wanda ya yi amfani da su domin cin zabe. Wadannan abubuwa guda biyu suna da matukar hatsari a cikin siyasar Nijeriya.
“Lallai wadannan abubuwa guda biyu suna da matukar tsari ga siyasar Nijeriya a halin yanzu,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp