Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya gabatar da naira biliyan 140, ga majalisar dokokin jihar, domin ta amince a matsayin kadafin kudin shekara mai zuwa 2021.
Da ya ke gabatar da kasafin ga majalisar gwamna Fintiri, ya ce an kiyasta kashe 72,817,892,910.00, kashi 52 na kasafin kan manyan ayyuka, da kuma kudaden shiga naira biliyan 63,216,516,530, kashi 48 na kasafin.
Gwamna Fintiri, ya kuma yi bayani ga majalisar cewa gwamnati ta lura da tsawon lokacin shigar kudaden da’ake samu a tsarin manyan kasuwanni, kafin a iya samun kudaden gudanarwa a kasafin.
Ya ci gaba da cewa, “kammala dukkanin ayyukan da akeyi yanzu, rage wani abu daga cikin kasafin ka’iya kawo nakasu ga kammala ayyukan a 2021, wanda kuma shi ne manufar gwamnatinsa kyautatawa jama’ar jiha,” in ji Fintiri.
Ya ce, hukumar tara kudaden haraji ta jihar ta cancanci yabo, ta daukaka matsayin kudaden shiga na wata-wata da ta ke tarawa, duk matsalar annobar korona.
Gwamna Fintiri, ya kuma bada bayanai wasu ayyukan da gwamnatin ta gabatar da kasafin kudin shekara mai karewa (2020), ta bangaren ilimi, kiwon lafiya, tsaro, da gyara tsarin ma’aikata, samar da aiki ga matasa maza da mata.
Haka kuma gwamnan ya yi kira ga ‘yan majalisar da su lura su kuma amince da kasafin domin bukatun jama’ar jihar su ci gaba da morema gwambatin da ta bullo da tsare-tsare domin daukaka matsayi da rayuwar jama’ar Adamawa.