Adron Homes and Properties wani katafaren kamfani ne da ya yi fice wajen gina gidane da manyan tituna a kasar nan, kamfanin ya taya Nijeriya murnar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Kamfanin wanda ya yi fice wajen gine-gine, ya yi imanin cewar samar da gidaje da gine-gine masu inganci na daya daga cikin abubuwan da ke daga kima da darajar kasa.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Abuja-Kaduna
- Dan Majalisar Kano Ya Dauki Malamai 105 Aikin Wucin Gadi
Manufar kamfanin, shi ne samar da gidaje masu rahusa ga ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da matsayi ko ajin mutum ba.
Kamar dai yadda kamfanin Adron Homes yake da burin ganin Nijeriya ta ci gaba, wajen samar da kayayyakin more rayuwa, kamfanin ya yi ado da launukan tutar Nijeriya don nuna goyon baya ga Nijeriya.
Shugaban rukunin kamfanonin, Aare Adetola EmmanuelKing, ya yi amfani da wannan damar wajen taya al’ummar kasar nan murnar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, wanda a cewarsa “wanannan ba karamin abu alfahari ba ne.”
“A matsayinmu na kasa daya al’umma daya, muna da abubuwa da yawa da za mu yi godiya a tattare da su; duba da abubuwan da ke faruwa a duniya, tabbas dole mu yi godiya. Babu shakka, ba mu kasance inda muke so ba, amma yayin da dimokuradiyyarmu da ‘yancin kai suka samar mana ci gaba, abubuwa za su inganta a nan gaba.”
“’Yan Nijeriya wasu jigon rukunin mutanen da suka samar wa duniya ci gaba ta bangarori daban-daban a rayuwa, irin su fagen wasanni, harkar nishadantarwa da jarumai daga masana’antar fina-finai ta Nollywood da kuma fannin kimiyya da fasaha, wanda matasa da yawa ke baje kolin baiwarsu.”
Aare Adetola ya ci gaba da cewa. “Mu a gidajen Adron muna ganin ya dace mu yi murna tare da taya al’umma murna ta hanyar ba da rangwamen kashi 50 cikin 100 na duk gidajenmu a fadin kasar nan.
“Don taya al’umma murna Adron Homes ta kawo tsari don bai wa abokan huldarsa damar mallakar fili ko gida ta hanya mafi sauki wajen biyan kudi,” kamar yadda manajan rukunin kamfanin ya bayyana.