Babbar jami’ar jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta kudu, ta ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara a kan tafarkinta na zamanantar da kanta, kuma Afrika ta Kudu na ganin akwai dimbin damarmakin hadin gwiwa da Sin wajen inganta zamanantar da kanta.
Gwen Ramokgopa, wadda ita ce babbar ma’ajiya ta jam’iyyar ANC, ta ce dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC), ya cimma kyakkyawan sakamako ta hanyar shirye-shiryen hadin gwiwar moriyar juna.
- ’Yan Kasuwa Daga Kasashe Da Yankuna 119 Sun Halarci CIFIT Karo Na 24
- Dubban Jama’a A Isra’ila Sun Yi Zanga-Zangar Neman Amincewa Da Yarjejeniyar Hamas
Ta ce taron FOCAC, ya kasance wata muhimmiyar dama ta karfafa hadin gwiwar Sin da Afrika a bangarori da dama, musammam a bangaren bunkasa dangantakar tattalin arziki da cinikayya .
Taken taron wanda ya gudana daga ranar Laraba zuwa Jumma’a, shi ne “hada hannu domin inganta zamanantarwa da gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya bisa babban mataki.”
Ta ce idan ana son inganta zamanantar da nahiyar Afrika, akwai bukatar la’akari da albarkar tattalin arzikin nahiyar da yadda za a lalubo damarmakin ci gaba da nahiyar ke da shi, wanda ke nufin kirkiro kyakkyawan muhallin kasuwanci da inganta hidimtawa al’ummar nahiyar da amfana da sabbin fasahohi, ciki har da fasahohi masu tsafta da suka shafi makamashi da motoci masu amfani da lantarki, tana mai cewa, Sin ta kasance jagora a wadannan bangarori, don haka, akwai damarmakin da za a iya karfafa hadin gwiwa da ita don daukaka zamanantar da kasar ta Afrika ta Kudu.
Ta kuma yaba sosai da shawarwarin taimakawa nahiyar Afrika bunkasa ayyukan masana’antu da shirin Sin na zamanantar da aikin gona a Afrika da shirin hadin gwiwar Sin da Afrika kan horar da masu basira, wadanda kasar Sin ta gabatar.
A cewarta, Sin da Afrika ta Kudu mambobi ne na kungiyar BRICS, kuma wakilan kungiyar kasashe masu tasowa, don haka, hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a mabambantan dandamali, ya taimaka wajen kara sautin muryar kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)