Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
Gwamnan Neja, kuma shugaban kungiyar gwamnonin Neja, Abubakar Sani Bello ya taya sabon sarkin Kagara, Alhaji Ahmed Garba Gunna murnar samun sarautar a matsayin sarkin Kagara na uku.
Nadin Ahmed Garba Gunna ya biyo bayan rasuwar tsohon sarki Alhaji Salihu Tanko wanda ya rasu 2 ga watan Maris din wannan shekarar akan gadon sarautar Kagara.
Alhaji Ahmed Garba wanda ya samu kuri’u mafi rinjaye daga masu jefa kuri’ar na zaben sarkin daga masarautar Kagara wanda aka tabbatar da shi a matsayin zababben sarkin a yau.
A bayanin gwamnan, ya bayyana nadin na sa a matsayin mafi cancanta da ‘yan majalisar masarautar su ka yi na tabbatar da cewar zai iya kai masarautar ga kyakkyawar matsayi.
Gwamna Sani Bello ya bayyana yakininsa ga sabon sarkin na kwarewarsa kuma mai yiwa jama’a hidima, da cewar sabon sarkin yana da kwarin guiwar cigaba da gina gurabun alheri daga wanda ya gada ta hanyar hadin kai majalisar masarautar.
” Zaben ka, bayan rike sarautar dan Majen Kagara, akan wannan kujerar ya bada tabbacin da ake da shi a kan ka kuma dukkanin al’ummar masarautar za ka samar masu walwala ta hanyar cigaba da gina kyawawan al’adun masarautar da al’adun jama’ar masarautar”.
Gwamnan ya tunatar da sabon sarkin da cewar ya samu wannan damar ne a mafi kalubalen lokaci da ake fama da matsalar tsaro a yankinsa, ya nemi yayi anfani da lokacin da dukiyarsa ta hanyar hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen samar da zaman lafiya a masarautar.
Gwamnan yayi kira ga al’ummar masarautar Kagara da su goyawa sabon sarkin baya wajen samun zaman lafiya dan bunkasar tattalin arzikin da cigaba musamman a jihar Neja.
Kafin nadin sabon sarkin, dan Majen Kagara, shi ne shugaban riko na hukumar tara harajin jihar Neja.