Yayin da zaben shugaban kasa ke kara karatowa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce akwai hatsarin gaske ‘yan Najeriya su mika mulki ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu; da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.
Tsohon mataimakin shugaban kasar nan, ya bayyana haka ne a taron kungiyar tattalin arzikin Nijeriya NESG a taron tattaunawa kan tattalin arziki da aka gudanar a Legas a ranar Litinin.
- Yadda Kannywood Ta Shiga Alhinin Rasuwar Jarumin Barkwanci, Kamal Aboki
- Atiku Ba Ya Tsoron A Bincike Shi – Dino Melaye
Ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da samun koma baya saboda gazawar gwamnatin APC.
A cewarsa, arzikin man fetur da iskar gas a Nijeriya ya ragu tun bayan bullowar gwamnatin APC.
Ya bayyana cewa Peter Obi bai da kwarewa wajen tafiyar da mulkin Nijeriya.
“Kwarewa yana da muhimmanci, kuma dole ne mu guje wa kurakuran da suka gabata.
Yana da matukar hatsari ga ‘yan Nijeriya su mika makomarsu ga ‘yan kore ko kuma ga shugaban jam’iyyar na kasa wanda ya kawo mu ga wannan halin da muke ciki,” in ji shi.