Gamayyar Matasan Arewa Mazauna Kudancin Nijeriya reshen Jihar Legas ta ankarar da Gwamnatin Jihar Kano a kan ta mike haikan wajen bankado bakin da ke kwararowa jihar da sunan neman mafaka, inda ta ce akwai babbar barazana game da hakan.
Shugaban gamayyar, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya yi kiran a zantawarsa da LEADERSHIP Hausa a tsakiyar makon nan.
- Kashi 31 Na ‘Yan Nijeriya Ba Su Iya Karatu Da Rubutu Ba ― Gwamnatin Tarayya
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
Shugaban gamayyar ya ce yadda mutanen Kano suka saki jiki ana sayar da filaye da gidaje barkatai ga bakin da ba a da wasu cikakkun sahihan bayanai a kansu abin tambaya ne, inda ya yi kira ga musamman jami’an tsaro na ‘yansanda da ‘yansandan sirri (DSS) da sauran wadanda abin ya shafa su rubanya kwazonsu domin bankado daga cikin bata-garin da ke ungulu da kan zabo da sunan baki.
“Muna kira da farko ga Gwamnatin Jihar Kano ita kanta, sannan ‘yansanda da ‘yansandan sirri na DSS da suran jami’an tsaro da lallai su sa ido a kan bakin da suke zuwa Jihar Kano domin neman mafaka.
Akwai babbar matsala dangane da hakan, shi ya sa ya zama dole mu yi kira ga gwamnati ta dauki mataki, sannan kuma mu fito fili mu yi wa al’umma bayani domin su sake nazari.
“Yadda ake bari baki daban-daban suke mallakar gidaje da kafa sababbin unguwoyin birni da kewaye wadanda ba za a tantance su ba, illa da zarar mutum ya zo ba a san inda ya fito ba a ba shi haya ko a sayar masa da fili ko gida, ya kamata gwamnati ta sanya idanu a kan wadannan al’amuran kuma muna kira de da gwamnatin da ta ja kunnen masu unguwanni da hakimai da dagatai da sauran shugabanni al’ummar Jihar Kanon baki daya a kula sosai. Allah ya ba mu zaman lafiya saboda Manzan Allah, Annabi Muhammadu (SAW),” In ji Galadanci.