• English
  • Business News
Monday, June 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo

by Rabi'at Sidi Bala
2 days ago
in Taskira
0
Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba kawo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamatakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi matasa, mafi yawa a yanu matasa na saurin bayyana aurensu tun kafin auren ya gabato, ta hanyar bude group domin tattaunawa game da auren wanda ake yi wa lakabi da ‘Sabe the date’, a yayin da wasu ke ganin hakan sam! Ba wayewa ba ce face ma matsala.

  • Hadin Gwiwar Sin Da Kasashe Masu Tasowa Ya Dade Da Zama Kan Gaba A Bangaren Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Waje
  • Zulum Ya Ba Da Tallafin Karatu Ga Mata ‘Yan Asalin Jihar Da Suka Samu Maki 250 A JAMB

Wannan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko mene ne alfanun hakan?, ko akwai wani kalubale da ka iya afkuwa game da hakan?”.

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Jamila Yahaya Jihar Katsina:

Labarai Masu Nasaba

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

Sam-sam hakan ba shi da wani alfanu domin yana kawo matsaloli da dama wanda babu lokacin lissafosu. Kalubalen da ka iya afkuwa kuwa shi ne; wadansu ‘yan matan ba sa tan-tance wadanda za su sa da wadanda ba za su saka ba, har da masu saka ‘yan’uwan miji, kawaye da ‘yan’uwa na cikin dangi duk a bi a cakuda su guri guda, kuma ba sa yin komai a lissafance ba sa tunanin a cikin yawan al’umman da ke ciki har da shaidani ciki ba, dan akwai wacce abu ya faru da ita daga bude group na biki (sabe the date) abu ya dawo babbar rigima har ta kai ga ‘police station’ kuma ba komai ya kawo hakan ba sai rarrabuwar ra’ayoyi daya ta zazzagi daya, ita ma dai wannan ya jawo mata babbar mastsala. Su masu wannan bidi’ar sun dauki cewar shi wannan bude group din wayewa ce gara su ma su yi ai lokacin sune, su yi hattara basu san hakan hanya ce ta samun matsalolli tsakanin kawaye, ‘yan’uwa da abokan arziki, su gane cewar su iyayenmu da kakanninmu da basu bude group-group din ba kuma babu shi ma a lokacinsu me ya ci su kuma me ya faru da zamantakewar aurensu face ma zaman lafiya da kuma samun zuri’a ta gari.

Sunana Hassana Tijjani Daga Gombe Najeriya:

Alfanun hakan shi ne yana hada kan juna a zama tsintsiya daya-madaurinki daya. Kuma hakan na nuna kulawa da nuna muhimmancin juna, kowa ya bada tashi gudmmawa da shawara aka ce “hannu da yawa maganin kazamar miya”, kuma a tsara biki mai kyau na gani na fada na bugawa a jarida. Tun da har kimiya da fasaha ta kawo wannan ci gaban me ya sa ba za ayi amani da shi ba Wadansu daga cikin ‘yan’uwa da abokan arzikin ba su da lokaci na samu a hadu guri guda don a tattauna don yanzu kowa ya kama sana’a in baka aikin ofis to, kana siye da siyarwa da haka a samu damar tattaunawa da mutum a duk nisan inda yake, don haka ba na ganin wa kalubale game da hakan, dan akan kanka ma in ka dubi bikin da dana yanzu kai ma ka san akwai babban bambanci. Shawarar da zan bawa su masu yin hakan su yi lokaci ne wataran ba nasu bane na ‘yan’yansu da jikokin sune. To ma idan ba a bude groups din ba ta wacce hanya a ke so a tsara bikin yadda zai tafi yadda ake bukata?, dan nasan akwai masu cewar hakan ka iya kawo rigima, ita ai ta san wanda ta kawo da inda ta nemo su dan haka kuwa duk abin da ya je ya dawo ita ce a ciki.

Sunana Hafsat Sa’eed Daga Naija:

Abin da na fahimta da bude group din da mata ke yi lokacin aurensu shi ne; suna saka masoyansu da ‘yan’uwa da abokan arziki, idan za a yi anko sai a saka ankon da account da duk wanda zai yi ankon ya tura kudin shi a hada wuri daya, in ba haka ba wasu ma ba lallai su sani ba. Ni dai a gare ni yin hakan yanada kyau saboda masoyanka ka tara kuma abun farin ciki ne, duk da cewa wasu na ganin idan mutum ya je ya yada yadda duniyar nan ta zama sai ya zamo matsala yanzu mutane boye aurensu suke yi sabida mugayen da za su kai ga sun raba aurenka. Kalubalen da ake iya samu wasu za sy iya kokarin ganin sun bata ka ko sun bata auren musamman idan aka san wanda za ka aura. Shawarar da zan bayar shi ne mutum ya zauna a yadda yake ya boye auren shi ya fi akan ya rika tallatawa gara a ji ranar daurin aure yadda zamani ya sauya.

Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Kaduna:

Wasu in suka bude group na kawaye ne wanda za su fadi komai na game da bikin ba sai an kira a waya ba suna gani ya fi sauki, gaskiya wasu da an saka su cikin group na kawaye amarya kalubale na farko shi ne turo da wani abu da bai shafi bikin ba da kayi magana kan haka sai abu ya zama fada. Shawara ta in har za ki bude group irin haka ya zama kawar amarya kawai ce za ta iya magana a cikin Allah ya sa mu dace.

Sunana Princess Fatima Mazadu:

Akwai amfanu gaskiya saboda za a yi ‘sharing idea’, sannan kuma za a samu daidaiton ra’ayi. Eh! akwai gaskiya saboda a wani lokacin har akan yi fada ko samun wasu kananun fitintinu, musamman bangare na mata, wadannan za su ga wanda aka yarda da zabinsu sune na gaban goshi wani lokaci gaba ma sai ta kullu. Shawara dai suna yi da taka tsamtsan saboda gujewa fitina da kananan maganganu.

Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To magana ta gaskiya ni a ganina ba shi da wani amfani ko muhimmancin, domin hasali ma rashin kunya ne, domin kuwa a al’ada ta Hausawa mata suna da kunyar da ba za su iya fadar bikin su. Kwarai kuwa akwai kalubale, domin da farko rashin kunya ne, domin ita al’adar malam bahaushe akwai kunya don haka bai dace ba mace take fadar bikin ta. To shawara ta a nan ita ce; ya kamata gaskiya su daina domin rashin kunya ne, ita kuma kunya tana da matukar muhimmanci a rayuwar ‘ya mace domin ado ce, don haka duk lokacin da mace ta rasa kunya to ta rasa komai a ruyawar ta.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:

Alfanun hakan zai kara tunasar da duk wanda wannan auren ya shafa domin ayi bikin cikin tsari. A nawa fahimtar babu wani kalubale sai dai ma ya kara bada damar duk wani shiri ayi shi cikin tsari da kuma magance biki ya zo ki ji ana cewa abu kaza da kaza ba a san da shi ba kuma gashi an riga da an makara. Su cigaba da hakan indai domin ayi bikin ciki tsari ne ba ma iya mata ba har da maza hakan zai kara kawo hadin kan al’umma, domin a irin wannan ne ake iya tsara kowa da irin duk wata rawa da mutane za su taka wajen gudanar da tsarin bikin ta inda koda za a yi abin da bai dace ba tun kafin lokacin za a kawo gyara Allah kasa mu dace.

Sunana Muktari Sabo Jahun Jihar Jigawa:

Bude group don tattaunawa akan abin da ya shafi biki tare da ‘yan’uwa da abokai hakan ba laifi bane sai dai idan abin da za a tattauna ya sabawa shari’a da al’ada. Kalubale na iya afkuwa musamman idan group din ya zama ana yin abin da ya sabawa shari’a da al’ada akan koyi abubuwa munana ta irin wannan hanyar kuma ta irin wannan hanya mata ke bayyana sirrin mazajensu da duk wani abu dake faruwa a tsakaninsu da mazajensu wanda hakan ba daidai bane. Shawara ita ce mata su ji tsoron Allah su sani duk abin da suka aikata ta wannan kafa dama kowacce Allah na ji na ganinsu kuma zai musu hisabi akan duk abin da suka aikata.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Aure
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Za Ki Hada Funkasonki

Next Post

Yadda Jarumai A Masana’antar Kannywood Ke Auren Junansu

Related

Taskira

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

1 week ago
Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
Taskira

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

1 week ago
Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu
Taskira

Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu

4 weeks ago
Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?
Taskira

Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?

1 month ago
Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
Taskira

Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma

2 months ago
Mece Ce Makomar ‘Ramadan Basket’ A Wannan Lokaci Na Matsin Tattalin Arziki?
Taskira

Mece Ce Makomar ‘Ramadan Basket’ A Wannan Lokaci Na Matsin Tattalin Arziki?

3 months ago
Next Post
Yadda Jarumai A Masana’antar Kannywood Ke Auren Junansu

Yadda Jarumai A Masana'antar Kannywood Ke Auren Junansu

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu Domin Bukukuwan Sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu Domin Bukukuwan Sallah

June 2, 2025
Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya

Hadin Gwiwa Hanya Ce Madaidaiciya Wajen Kiyaye Tsaron Shiyya

June 2, 2025
Malaman Jami’ar Gombe Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani 

Tsaro: ‘Yansanda Sun Kulle Tashar Dadin Kowa Da Sauransu A Gombe 

June 2, 2025
Mataimakin shugaban kasa

Shettima: Shekaru Biyu Na Mataimaki, Jagora Mai Hangen Nesa Da Kawo Sauyi Nagari

June 2, 2025

AlÆ™alai Da Lauyoyi Sun Yi Cirko A Gaban Kotu Bayan Fara Yajin Aikin Ma’aikatan Shari’a

June 2, 2025
Babu Wanda Zai Iya Kora Ta Daga PDP —  Wike

Babu Wanda Zai Iya Kora Ta Daga PDP —  Wike

June 2, 2025
Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya

Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya

June 2, 2025
Jirgin Sojoji Yayi Kuskuren Buɗe Wuta Kan Ƴan Sa Kai A Maru

Jirgin Sojoji Yayi Kuskuren Buɗe Wuta Kan Ƴan Sa Kai A Maru

June 2, 2025
Ɗaliban Northwest Kano Sun Yi Zanga-Zanga Kan Ƙarin Kuɗin Makaranta

Ɗaliban Northwest Kano Sun Yi Zanga-Zanga Kan Ƙarin Kuɗin Makaranta

June 2, 2025
Manchester United Ta Kammala ÆŠaukar Cunha Daga Wolves Akan Miliyan 62.5

Manchester United Ta Kammala ÆŠaukar Cunha Daga Wolves Akan Miliyan 62.5

June 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.