Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa (NJS), ta kafa kwamiti 15 da za su binciki zarge-zargen aikata rashin da’a da wasu alkalai guda 15 na manyan kotun tarayya da na jiha suka yi.
Kwamitin za su bibiyi tare da bincikar hakikanin zarge-zargen da ake wa alkalan ta hanyar korafe-korafen da aka shigar a kansu daga wajen daidaikun mutane, kungiyoyi da hukumomi domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
- Yahaya Bello Da Wike Sun Yi Ganawar Sirri A Ribas
- An Gina Katafaren Masallacin Da Ya Fi Kowanne Girma A Duniya
A wata sanarwar manema labarai da daraktan yada labarai na NJC, Mista Soji Oye ya fitar jiya a Abuja, ya ce, an cimma wannan matakin ne a zaman majalisar karo na 99 karkashin jagorancin babban joji na kasa (CJN), mai shari’a Olukayode Ariwoola.
Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan gabatar da shawarwarin wasu kwamitim tantance korafe-korafe guda uku da suka yi la’akari da koke-koke 66 da majalisar ta aike musu a fadin tarayyar kasar nan.
Sai dai sanarwar ba ta jero sunayen alkalan da za su fuskanci binciken ba tare da yankunan da suke ko irin laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
Ko da yake tuni majalisar ta sanya kafa ta shure korafe-korafe guda 51 da ake zargin alkalan kotunan tarayya da na jihohi bisa gaza hujja ko tabbaci da har zai sanya a tuhumi aikalai ko kuma batun an daukaka kararsa ko kuma sakamakon cewa alkalan da batun ya shafa sun kammala wa’adin aikinsu.