An karbo daga Abdullahi bin Abbas (RA) cewa ma’anar Yaasiyn tana nufin “Ya kai Dan Adam cikakke, tana nufin Annabi Muhammadu (SAW)”. Manzon Allah (SAW) Dan Adam ne cikakke. Har ila yau Abdullahi bin Abbas (RA) din ya fada a ruwayarsa cewa Yaasiyn tana nufin rantsuwa ce da sunan Annabi. Kuma tana daga cikin sunayen Allah. Allah ya dauki sunan ya baiwa Manzon Allah (SAW). Mun taba yin bayani kan sunayen Allah da Allah Ta’ala ya baiwa Manzon Allah (SAW) a wani darasinmu da ya gabata, irin su Ra’ufu da Rahimu.
Malam Dajjaju (Malamin Larabci, mutumin Bagadad) ya ce kila an ce ma’anar Yaasiyn tana nufin sunan Manzon Allah ne kai tsaye, wato ‘Muhammadu’ (SAW). To idan haka ne, kalmar ta Yaasiyn daga yaren Siriyananci ne; yaren Annabi Ibrahim (AS) kamar irin su ‘Ahiyyan Sharahiyyan’ da ke nufin ‘Hayyun Kayyum’, Manzon Allah (SAW) ya fade su. To ita ma kalmar Yaasiyn tana daga cikinsu, ma’anarta da larabci ita ce ‘Muhammadu’ (SAW), idan an koma Siriyananci kuma sai a ce ‘Yaasiyn’.
- Allah Ya Yi Rantsuwa Da Girman Darajar Manzon Allah S.A.W (1)
- Allah Ya Amintar Da Zuciyar Manzon Allah (SAW) Tare Da Tausasawa
Kila kuma aka ce ma’anarta (Yaasiyn), tana nufin ‘Ya kai cikakken mutum’. Kila kuma aka ce tana nufin ‘Ya kai Dan Adam cikakke’, wanda ya fadi wannan ya yi daidai da fassarar Abdullahi bin Abbas (RA). An karbo daga Sayyidina Muhammadu Dan Hanafiyyatu (Dan Sayyidina Aliyu Karramallahu wajhahu ne. Bayan rasuwar Sayyada Fadimah (AS), Sayyidina Aliyu ya yi aure da yawa. Lokacin da aka yi Yakin Musulaimatul Kazzab Sayyidina Aliyu ya samu kuyanga ‘yar kabilar Hanafiyyah, ita ce ta haifi shi Muhammadul Hanafiyya. Bai fi shekara biyu da wafatin Annabi SAW ba aka haife shi sai Sayyidina Aliyu ya sanya masa sunan Manzon Allah SAW. Akwai bayanai da yawa a kansa kamar sauran ‘yan’uwansa) cewa ma’anar Yaasiyn tana nufin ‘Ya Muhammadu’ (SAW). Ka ga a nan, Sayyidina Muhammadul Hanafiyya da Malam Dajjaju fassararsu ta zo daya cewa Kalmar Yaasiyn tana nufin ‘Ya Muhammadu’.
An karbo daga Malam Ka’abul Ahbari cewa ma’anar Yaasiyn rantsuwa ce da Allah ya yi (da Kalmar) tun kafin ya halicci sama da kasa da shekara dubu biyu. Kila haka ya gani a cikin Attaura. Malam Alkadiy Iyad ya ce to idan an kadarta cewa ‘Yaasiyn’ na daga cikin sunayen Manzon Allah (SAW) kuma karatu ya inganta cewa rantsuwa ce, to za a gane akwai girmamawa cikin wannan maganar dangane da abin da ya rigaya da Allah Ta’ala ya ce ya rantse da rayuwar Manzon Allah (SAW). Wato ma’anar haka, Allah ya rantse da rayuwar Manzon Allah kuma ya rantse da sunansa (SAW) kana ya tabbatar da cewa Annabi Muhammadu (SAW) Manzonsa ne (SWT) kamar yadda ya zo a farko-farkon Suratu Yaasiyn. Dama akwai wurare da dama da Allah (SWT) yake jera rantsuwa a cikin Alkur’ani. Kamar yadda muka gani a nan ya rantse da Alkur’ani kana kuma ya rantse da rayuwar Manzon Allah (SAW). Wannan magana tana karfafuwa sosai saboda Allah ya dora rantsuwa kan rantsuwa ta hanyar amfani da harafin ‘wawun na adafi’ (harafin sada kalma). Daga nan sai aka fahimci cewa lallai ayar farkon (Yaasiyn) ita ma rantsuwa ce.
Idan kuma an ce Allah ya kira sunan Manzon Allah ne, ma’ana ya ‘Yaasiyn’ da ke nufin ya Muhammadu ko sauran fassarar sunan da muka kawo bayanansu a baya; to Allah ya zo da wata rantsuwa kuma bayan haka domin tabbatar da Annabcinsa (SAW). Allah ya kira sunansa an ji shi kuru-kuru sai kuma ya rantse don tabbatar da Manzancin Manzon Allah (SAW) da shaidawar cewa Manzon Allah shiryayye ne (a ayar da Allah ya ce kai kana daga cikin Ma’aika kuma a kan tafarci madaidaici). Ubangiji maigirma da daukaka ya rantse da sunan Manzon Allah da Littafinsa (Alkur’ani) cewa shi Manzon Allah yana daga cikin Ma’aika bisa wahayin da ya yi masa zuwa ga bayinsa. Kuma bayan Manzon Allah yana daga ciki Ma’aika har ila yau yana kan hanya madaidaiciya daga imaninsa, ma’ana yana kan hanyar da babu karkata a cikinta a kan gaskiya.
Malam Nakkashu ya ce Allah bai rantse a kan kowa daga cikin Annabawa kan manzancin da ya aiko su da shi ba a cikin Littafinsa (Alkur’ani) sai Manzon Allah (SAW). Kowane Manzo da aka aiko idan mutanensa sun karyata shi; shi Manzon da kansa ne yake basu amsa. Amma da kafiran Annabi Muhammad (SAW) suka karyata shi Allah ne da kansa ya rantse kusan sau shida ya ce lallai shi (Annabi Muhammadu) Manzonsa ne. Allah ba ya sa wasa a cikin komai nasa, koda bai rantse ba kawai amsa ya bayar cewa Annabi Muhammadu Manzonsa ne ya isa amma kuma saboda karfafa abin sai ya yi ta zubo rantsuwa. A wata fahimtar kuma aka ce dalilin da ya sa Allah ya yi rantsuwar a kan tabbatar da Manzancin Annabi (SAW) shi ne: a Shari’ar da ya saukar ma wannan al’umma ya umurci mai kare kansa a gaban shari’a ya yi rantsuwa. To tunda kafiran Makka sun karyata Manzancin Manzon Allah (SAW), a maimakon shi ya yi rantsuwa don kare Manzancin nasa sai Allah da kansa ya yi hakan saboda girman darajar Manzon Allah a wurinsa (SWT). Wannan duka ya tafi a bisa salsalar fassarar da aka yi wa ‘Yaasiyn’ a matsayin ‘Shugaba’. Kuma Wannan din ya tabbata a cikin Hadisi ingatacce wanda Manzon Allah (SAW) ya ce “Ni ne shugaban Dan Adam duka kuma ba alfahari nake ba (ina gode wa Ubangijina ne).
Wata ayar kuma da ke nuna rantsuwar da Allah ya yi da Manzon Allah (SAW) ita ce farkon Suratul Balad.
Harafin ‘Laa’ da ta zo a farkon ayar wasu malamai musamman Malam Makkiy sun fassarata da cewa Allah (SWT) yana nufin “Ba domin kai (Ya Rasulallah) kana cikin wannan garin ba; ba zan rantse da shi ba”. Ko kuma “Ina rantsuwa da wannan garin ne saboda kana ciki amma idan ka fita daga cikinsa ba zan rantse da shi ba”. A wata aya ta cikin Suratun Nisa’i Allah ya nuna a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya fita daga garin (Makka) ya koma Madina kamar shi ma (SWT) ya koma can. Domin ayar ta ce “…duk wanda ya fita daga gidansa yana mai yin Hijira zuwa wurin Allah da Manzons”. A Akidarmu Allah yana ko ina amma kuma babu kamar inda Masoyinsa Manzon Allah (SAW) yake. Wannan ai ya isa girman Manzon Allah, Allah ya ce ba zai rantse da Makkah ba idan ba ya ciki (kamar yadda wannan fassarar take nuni).
Kila kuma an ce wannan harafin na ‘Laa’ kara magana ne. Muma a Hausa muna da irin wannan. Kamar misali wani zai ba da amsa kan wani abu da aka tambaye shi ko ya aikata wani abu? Sai ya ce “a’a, ban yi ba ko a’a wallahi ba zan yi ba”. Duk wannan (a’a) kari ne. To kila wannan ‘Laa’ din karin magana ne. Don haka ma’anar ayar tana nufin Allah yana cewa “ina rantsewa da wannan garin. Idan kana ciki”. Wato Allah zai rantse da Makkah Idan Manzon Allah (SAW) yana ciki. Ko kuwa Allah ya ce “zan rantse da wannan garin saboda kai (SAW)”. Ko kuma ba zaman Manzon Allah a Makka Allah yake nufi ba (a ayar), Allah yana nufin ya halatta wa Manzon Allah garin na Makkah domin ita haramun ce ga kowa. Ko da gini mutum zai yi sai ya kasance akwai wata bishiya da yake so ya sare, ba zai sare ba sai an yi masa kudin fansa ya biya. Haka idan aka kashe dabba. Kamar misali mutum ya kashe bauna to dole sai ya biya da saniya. Sai dai za a iya karya baure kamar yadda Abbas (RA) ya tambayi Manzon Allah (SAW) a kai ya amince a yanke. Koda laifi mutum ya yi ya shiga yankin da Allah ya haramta ba za a shiga ciki a kama shi ba sai dai a yi masa talala, kamar a hana shi abinci har yunwa ta koro shi ya fito daga ciki saboda girman Makkah. To amma Manzon Allah (SAW) aka halatta wa ita. Shi ma ya ce na awa daya ne tak a lokacin da za a yi Fatahu Makkata. Wannan duka saboda fito da ma’anar yadda wasu suka fassara ayar ta biyu ce mai kalmar ‘hillu’ da cewa ana nufin hallata garin ne ga Annabi (SAW) ba zamansa a ciki ba, kamar yadda malaman da suka tafi a kan wannan Tafsirin suka bayyana.