Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Al’umman Birshi Sun Zargi Kamfanin Triacta Da Kuntata Wa Rayuwarsu

Published

on

Al’umman kauyen Birshin Fulani da ke cikin kwaryar Bauchi sun koka da yadda kamfanin ‘TRIACTA’ ke kuntata wa rayuwarsu ta hanyar fasa nakiya domin sarrafa kwalta da duwatsu.

Mazauna kauyen sun yi zargin cewar rayuwarsu na fuskantar hatsari a duk ranar da kamfanin ya tashi harba nakiyarsa domin yin aiyukan da ke gabansa, inda suka ce kamfanin yayi matukar kusa-kusa da cikin al’umma, a bisa haka hayakin da kamfanin ke fitarwa a kullum rana na barazana wa lafiyarsu sai suka nemi daukin hukumomin da abin ya shafa.

Muhammad Auwal Ibrahim, daya daga cikin mazauna kauyen, ya shaida wa manema labaru cewa, “Shi wannan kamfanin na Triacta gaskiya ba mu jin dadin aikinsa a garinmu. Suna aikin nika duwatsu da kwalta ne a nan din. A kowani lokaci hayakin na tasowa yana hawa kan jama’a. A bisa haka jama’anmu da dama sun samu matsala kala-kala a sakamakon hakan.”

Ya ce, lokaci-lokaci ne kamfanin ke wannan aiki, inda ya kara da cewa “Wani lokacin sukan harba nakiya sau uku a wata, wani lokacin bai kaiwa hakan.”

“Duk lokacin da za su yi sukan sanar da mu cewar mu tashi daga gidajenmu mu fita zuwa wani wajen. Idan suka sanar da a fita, mutum ya ki sukan iya wulakanta shi sosai.

“Hatta ni kaina, akwai wata rana za su harba nakiyarsu suka sanar da cewar kowa ya tashi ya fita, na tashi zan fita a bisa laifi na wai ban bar iyaka wurin da shi mutumin yake son na je ba, ya dauki Amsa-Kuwa (Lasifika) ya kwada min a tsakar Ka, wanda hakan ya jawo fashewar kai na.” A cewar Auwal.

Ya kara da cewa, sau tari sukan basu kamar mintuna 30 zuwa awa daya kafin su harba nakiyar, inda kuma ya ce masu aikin kamfanin sukan dauki tsawon kamar awa guda suna aikin harba nakiyar tasu.

Dangane da hayakin da yake tashi ya mamaye su Auwal ya ce, “A kullum sai wannan hayakin ya tashi mana. Illa kawai ranar Asabar da Lahadi da basu aikin. Amma a kowani rana sai sun turnuke mu da hakakin nan. A ranar Asabar da Lahadi kacal muke samun dan hutu daga shan hayaki.”

Ya yi karin haske da cewar a duk lokacin da kamfanin za su harba nakiyarsu, dole ne dukkanin gidajen da suke makwabta da wurin da kamfanin ke aikin sarrafa kwalta su tashi domin gudun cutarwa, “Gidajen da wannan abin yake shafa duk lokacin harba nakiyar nan sun kai 20 ko ma fiye.” A cewarshi.

Muhammad Auwal ya kuma ce, mafiya yawan wadanda hayakin ke cutarwa suna yawan fuskantar cutuka daban-daban, ya kuma ce kamfanin ya shafe sama da shekaru 10 na gudanar da aiyukansa a wannan wajen.

A gefe daya Muhammad ya shaida cewar sakamakon aiyukan kamfanin rijiyoyinsu da dama sun kafe ba tare da ci gaba da bada ruwa ba.

Shi ma Tukur Muhammad wanda ya ce shi haifaffen wajen ne, ya tofa albarkacin bakinsa kan batun da cewa, “Kamar yanzu yadda kuke kallon kura na tashi daga inda kamfanin ke aiki lallai mu yana cutar da mu sosai.

“Baya ga hakan, sukan buga nakiya wanda ke fasa mana dakuna wani lokacin yana fasa mana Shadda (Masai) da sauran kayyakinmu.”

Ya yi zargi cewar idan kamfanin ya lalata musu kayyaki a sakamakon harba nakiyarsa bai zuwa ya gyara musu yadda ya dace illa su dan like ginin da suka fasa kadan, “Nakiyarsu ya taba tsaga min daki amma abin da aka yi min na gyara bai taka-kara ya karya ba, karshe dai nine na gyara kayana. Don haka basu gyara mana wuraren da suka lalata mana yadda ya dace, da yawa hakan ya shafesu,” a cewarshi.

Ya kara da cewa a lokacin da kamfanin ya fara jefa nakiyarsa sun nuna rashin amincewarsu kan aikin kamfanin amma daga karshe kukansu bai kai ga samun tagomashi ba.

Daga bisani ya ce suna bukatar gwamnati da kungiyoyin da abin ya shafa da su shigo cikin lamarin tare da tsawatar wa kamfanin domin a samu gyara.

Inda ya ce suna bukatar kai tsaye kamfanin ya tashi daga inda yake gami da neman wani kurin domin su kam suna cutuwa matuka.

Tukur Muhammad ya ce muddin kamfanin zai ci gaba da harba nakiya wanda ke firgitasu to lallai basu bukatar hakan ya ci gaba da faruwa da su. Sai ya nemi a samar da dauki na gaggawa domin gyara lamarin.

‘Yan jarida sun nemi bangaren Hakimai iyayen kasa domin jin ta bakinsu, inda Alhaji Isah Chiroman Birshi ya ce suna sane da korafe-korafen jama’arsu.

Daga bisani sai ya ce domin daidaita lamura, kamfanin ya dauki Bala na unguwar Galambi da aka daura wa alhakin shiga tsakanin jama’a da kamfanin ta fuskacin tattara korafe-korafensu.

“Idan kamfani ya zauna a cikin jama’a dole ne ya zama suna cutuwa. Mu na son kamfanin nan ya kara kokarin kyautata wa makwabtan da yake aikinsa a kusa da su. Duk kuma wanda abinsa ya baci a kowani lokaci su yi kokarin gyara masa ko ma fiye da abin da aka lalata masa da farko. Yin hakan zai kara samar da fahimtar juna a tsakanin kamfanin da jama’a,” a cewar Chiroman.

Isa Chiroma ya kara da cewa a duk lokacin da wata kamfani ke aiki a cikin wata al’umma to takan yi wasu aiyukan bunkasa wannan yankin, “A da baya can kamfanin nan sun yi aikin taimakon jama’a na gina titi mai nisan kilomita daya. A sakamakon rashin sanin dokokin sai ya zama mun dauki tsawon shekara tara ba mu sake tuntubarsu domin sake sabunta yarjejeniyar ba. Daga baya sai muka samu bayani daga wakilin ma’aikatar muhalli ta tarayya da ke shaida mana cewar irin wannan yarjejeniyar ana sake sabunta shi duk bayan shekara biyar. Nan take mu ka nemi kamfanin domin a sake zama. Kuma an sake cimma matsaya kan hakan.

“A bisa hakan sun sake bada tallafin naira miliyan biyu domin gina azuzuwa guda biyu wanda har yanzu dai ba a kai ga kammalawa ba,” in ji Isa.

Basaraken ya kuma ce, aikin da kamfanin ya bayar na gudana ne a karkashin shugaban kungiyar ci-gaban Birshi.

Ya kuma ce, kauyen nasu na bukatar ababen more rayuwa da suka hada da fanfo, fanfon tuka-tuka, asibitoci, makarantu, wuta mai amfani da hasken rana da sauransu.

Chiroman Birshi ya kuma bayyana cewar kamfanin na daukan matasan garin aikin leburanci sai dai kamfanin bai amincewa ya daukesu babban aiki mai tsoka.

Kan wanda aka fasa wa kai kuwa, ya ce dukkanin matakan da suka dace na sasanta lamarin tunin su ka yi.

Dangane da bukatar jama’an garin na cewar kamfanin ya tattara komatsansa ya bar garin nasu, Masarautar kauyen ta ce; “A shugabance ba wani alfanun da muke samu na zamansu a nan wanda talakawanmu bas u samu. Don haka tashinsu ba wani damuwa bane a garemu,” Inji Isa Chiroman Birshi.

A gefen kamfanin da ake aikin shimfida titi na ‘TRIACTA’ kuwa, ‘yan jarida sun shafe tsawon awa daya zuwa biyu domin jin ta bakinsu, amma kamfanin ya ki cewa uffan kan zarge-zargen da jama’an garin suka masa har zuwa lokacin aiko da rahoton nan. Inda Turawan da suke wurin suka ki amsa tambayoyinmu. Idan mun samu martanin kamfanin za mu shaida wa duniya.

Wakazalika, ‘yan jarida sun kuma nemi jin ta bakin kwamsishinan ayyuka na jihar Bauchi Abdulkadir Ibrahim Cikasoron Bauchi amma hakarsu bai kai cimma ruwa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: