Auren da aka gudanar a Jahun, Jihar Jigawa, ya rikiɗe daga murna zuwa tashin hankali bayan zargin cewa amarya ta sanya guba a abincin da aka yi wa baƙi.
Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya, yayin da angon ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali. Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni na soma bincike.
- Mahaifiyar Gwamnan Jigawa, Umar Namadi Ta Rasu
- Ƙasa Da Sa’o’i 30 Da Rasuwar Mahaifiyarsa, Gwamnan Jigawa Ya Sake Rasa Ɗansa A Hatsarin Mota
“Mun samu rahoton cewa ana zargin amaryar da saka guba a abincin baƙi, wanda ya sanya angon cikin yanayi mai muni. An kama amaryar tare da wata mace guda, kuma suna hannun CID don bincike,”
In ji Adam.
Ya kara da cewa duka waɗanda suka ci abincin sun sha wahala sosai, banda wanda ya mutu, an sallame su daga asibiti. Sai dai, ba a bayyana sunayen ango ko mamacin, ko kuma sauran waɗanda abin ya shafa ba.
Rundunar ‘yansanda ta sha alwashin ganin an gurfanar da duk waɗanda aka samu da hannu alamarin.